28 Faburairu 2025 - 13:58
Tashin Bom A Pakistan Yayi Sanadin Shahadar Mutane 6

Majiyar Pakistan ta rawaito cewa akalla mutane 6 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a lokacin sallar Juma'a a masallacin Haqqaniyyah dake arewacin kasar.

Fashewar fashe a birnin Quetta na kasar Pakistan ya yi sanadiyar jikkatar mutane da dama a sa'o'i kadan bayan mummunan harin kunar bakin wake da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan, 'yan sanda a Quetta, babban birnin lardin Balochistan, sun sanar a ranar yau Juma'a cewa mutane tara sun jikkata sakamakon fashewar wani bam a birnin.

A wannan harin An kashe ɗan shugaban Taliban na Pakistan

Maulana Hamidul Haq, wanda ya karbi ragamar shugabancin kungiyar siyasa ta Haqqani da cibiyar addini a Pakistan bayan kashe mahaifinsa Maulana Samiul Haq (wanda aka fi sani da mahaifin ruhaniyya na Taliban), an kashe shi a wani harin kunar bakin wake a yau.

An kai wannan harin kunar bakin wake ne a yau a cibiyar addini ta jama'ar Haqqaniyya da ke gundumar Akora-e-Khattak a lardin Khyber Pakhtunkhwa.

Jama'ar Haqqani na daya daga cikin shahararrun cibiyoyin addini na kungiyar Deyobandiyya, inda da yawa daga cikin shugabannin Taliban na Afghanistan da Taliban na Pakistan, ciki har da shugabannin kungiyar Haqqani suka yi karatu.

‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar wasu masu ibada a fashewar, inda suka ce mai yiwuwa harin kunar bakin wake ne.

An kashe Maulana Samiul Haq, wanda ya kafa kungiyar Haqqani kuma wanda aka fi sani da mahaifin ruhaniyya na Taliban, a wajen Islamabad a tsakiyar watan Nuwamba 2018. Inda a yau Aka kashe Maulana Hamidul Haq babban dan Maulana Samiul Haq a fashewar bam din na yau.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na kunar bakin wake na yau, sai dai wasu majiyoyi na cikin gida na cewa akwai yiwuwar kungiyar ISIS na da hannu a harin.