20 Faburairu 2025 - 19:08
Ranar Jana'izar Shahidai Sayyid Hasan Nasrallah Da Sayyid Safiyuddin Rana Mai Cike Da Juna Soyayya Da Baƙin Cikin Rabuwa Da Masoya

Fitattun masanan Lebanon a wata hira da wakilin ABNA a Beirut: Jana'izar Shahidai za ta kasance rana mai cike da tarihi da nuna soyayya da bakin ciki + bidiyo

Fitattun masanan Lebanon a wata hira da wakilin ABNA a Beirut: Jana'izar za ta kasance rana mai cike da tarihi da nuna soyayya da bakin cikin rabuwa da masoya.

Wasu fitattun masana na kasar Lebanon sun bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da suka yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlulbaiti (ABNA) a gefen taron kwamitin yada labarai na jana'izar Shahidai a birnin Beirut, game da halaye, da wajibcin gudanar da taron na musamman, da shirye-shiryen wannan jana'izar mai dimbin tarihi.

A kwanakin nan idanuwa da hankulan masoya da makiya gwagwarmaya a duniya da masu sa ido da manazarta na kasa da kasa sun fi karkata ne kan birnin Beirut da kuma tarukan jana'izar shahidan gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon, shahidai Sayyid Hasan Nasrallah da Sayyid Hashim Safiyuddin, taron da zai zamo wani lamari na tarihi da ke da muhimmanci daga bangarori daban-daban da kuma halin da ake ciki a kasar Lebanon.

Da dama daga masu sharhi suna ganin wannan rana a matsayin rana mai cike da tarihi ga kasar Labanon da yankin wanda masu goyon baya da masu adawa da gwagwarmaya a duniya suke ganin cewa dabi'un shahidai na siyasa da na kashin kai, musamman Sayyid Hasan Nasrullah, sun haifar da farin jini a cikin zukata, ta yadda wannan rana za ta zama rana mai daraja.

A wata tattaunawa ta musamman da wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (ABNA) a birnin Beirut, fitattun masana na kasar Lebanon, sun yi bayani kan halaye, da wajibcin gudanar da taron na musamman, da shirye-shiryen wannan jana'izar mai dimbin tarihi.

Ramzi Abdel Khaliq babban editan jaridar Al-Banna na kasar Labanon ya shaidawa wakilin ABNA a gefen taron manema labarai na jana'izar Shahidai Nasrallah da Safiyuddin cewa: Duk da irin mummunan rauni da muka sha, wanda mafi muhimmanci shi ne rashin Sayyid Hasan da Sayyid Hashem, mu ma mun samu gagarumar nasara. Sadaukarwar da 'ya'yan gwagwarmaya da kuma al'ummar kudancin Lebanon suka yi abu ne mai ban mamaki. Waɗannan sadaukarwa babu shakka za su kai ga nasara a nan gaba.

Wannan kwararre dan kasar Labanon ya kara da cewa: A fagen yada labarai, ko shakka babu adadi mai yawa na kafofin yada labarai, daga Labanon da wadanda ba na Labanon ba, daga cibiyoyin Larabawa da na kasa da kasa, za su dauki nauyin yada wannan lamari. Wannan babban lamari ne a wannan lokaci. Abin da kuke gani, shi ne matakan da kwamitin koli na shirya taron jana'izar ya dauka, wanda ya yi ta hanyar mai da hankali ga dukkanin 'yan jarida, da manema labaru, tare da samar da dukkanin abubuwan da suka dace da sufuri da kuma bukatun watsa shirye-shirye kai tsaye.

Shi ma babban sakataren cibiyar yada labarai da shiryarwa ta addinin muslunci ta kasar Labanon Sheikh Muhammad Al-Lababidi ya dauki ranar jana'izar a matsayin babbar ranar hadin kan kasa domin tabbatar da cewa ba za mu mika wuya ga makiya yahudawan sahyoniya ba, yana mai cewa: Wannan lamari ya wuce rarrabuwar kawuna na addini da na mazhaba. A yau, wannan taron ya zama na musamman ga dukan mutanen duniya masu daraja.

Ya bayyana cewa taron zai yi yawa sosai, ya kara da cewa: "Muna magana ne game da mahalarta fiye da miliyan daya da kuma kasancewar sama da mutane dari biyar a hukumance." A wurin jana'izar shahidan da kuma wannan ƙaramin yanki, halartar mutane sama da dari biyar zai zama abin ban mamaki.

Nasser Qandil, babban editan jaridar Al-Anbaa na kasar Labanon kuma daya daga cikin jami'an da ke kula da gudanar da taron jana'izar, ya kara da cewa: "An kafa wasu kwamitocin da ba na kafafen yada labarai ba, don tabbatar da tsari da shirya jana'izar a cikin gaggarumar hanya da kuma hana aukuwar al'amuran da ke haifar da karancin ayyuka saboda kwararowar dimbin mahalarta taron, kuma wadannan kwamitocin za su kasance da shirye-shirye da dama da ayyukansu.

Wannan fitaccen masani dan kasar Labanon ya kara da cewa: “Kara yawan masu shigowa domin halartar taron ba aikin kwamitin shiryawa bane. Wannan adadin na masu shigowa ya samo asali ne saboda sha'awar jama'a na son halarta don haka wannan manufa ba alhakin kwamitin ba ne, a'a, zukata ne za su gudanar da shi, za mu ga cewa dubban daruruwan mutane za su fito kan tituna saboda soyayya da sha'awar su. Manufar kwamitin ita ce hana cutarwa da za a iya samu daga yawan shiga da kuma cutarwa ga jama'a, da kuma magance rashin kayan aiki.

A karshe ya ce, "Na yi imani za mu shaida ranar nuna soyayya da nuna bakin ciki a tare". Wannan taro zai kasance na musamman a irinsa da ake gabatarwa.