Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta mayar da martani kan shahadar da wasu matasan Palastinawa uku a lokacin artabu da sojojin sahyoniyawan bayan da suka ki mika wuya a sansanin "Al-Fara'a" da ke gabar yammacin kogin Jordan, tare da sanar da cewa laifuffukan da gwamnatin sahyoniyawan ke aikatawa a yammacin gabar kogin Jordan ba za su iya girgiza azama da ƙarfin al'ummar Palastinu ba.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (A.S.) - ABNA- ya habarta bisa nakaltowa daga Kamfanin dillancin labaran Quds bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na Shahab cewa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fitar da sanarwar cewa, karuwar laifuffukan da yahudawan sahyoniya suke yi a yankin yammacin gabar kogin Jordan da kuma karuwar ayyukan barna da kashe-kashe na nuni da yunkurin maras nasara na Isra'ila kan al'ummar Palastinu, tare da ci gaba da kokarin da ba zai yi nasara ba na nufin dakile ci gaba da yaduwar gwagwarmaya a yankin yammacin kogin Jordan.
Kamfanin dillancin labaran Shahab ya kuma kawo cewa, har ila yau kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta ce: Muna taya shahidan Tubas da suka yi shahada a fafatawar da dakarun sa-kai na yahudawan sahyoniya, tare da jaddada cewa kisan gillar da aka yi wa mayakan na gwagwarmayar za su ci gaba da bayar da goyon baya da kuma kara dagewar al'ummar Palastinu a yammacin gabar kogin Jordan.
Har ila yau kungiyar Hamas ta kara jaddada cewa harin kisan gilla da aka yi a sansanin "Al-Fara" tare da harin da jami'an tsaron gwamnatin Falasdinu suka kai tare da kame wasu mayakan gwagwarmaya tare da lakada wa daya daga cikinsu duka, lamari ne mai hatsarin gaske wanda ke nuni da laifin hadin gwiwar tsaro tsakanin gwamnatin sahyoniya da shugabanin Palasdinawa na zubar da jinin Palasdinawa.
A karshen wannan bayani, kungiyar Hamas ta yi kira ga bangarori daban-daban na al'ummar Palastinu a yammacin gabar kogin Jordan da su tashi tsaye wajen yaki da duk wani makirci na ruguza al'ummar Palastinu tare da tallafawa dakarun gwagwarmaya a ko'ina.
An fitar da wannan sanarwa ne bayan da wasu mayakan Falasdinawa uku suka yi shahada a yammacin ranar Laraba bayan da aka kewaye gidansu da ke sansanin Al-Fara da ke kudu da Tubas a arewa maso yammacin gabar kogin Jordan, kuma an yi kazamin fada tsakanin mayakan gwagwarmaya da sojojin Isra'ila. Sojojin yahudawan sahyoniya sun yi wa gidan wani matashi mai suna "Yousef Tayyeh" kawanya a sansanin Al-Fara, lamarin da ya kai ga kazamin fada da makami tare da kai wa gidan harin bama-bamai.
Bayan da sojojin yahudawan sahyoniya suka tabbatar da cewa an kashe dukkan mutanen da ke cikin gidan sun kwace gawar shahidan uku tare janyewa da baya.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan sahayoniya suke yi kan mamaya a gabar yammacin kogin Jordan da birnin Kudus, ya yi sanadin shahadar Palasdinawa 915, da jikkata wasu kusan 7,000, tare da kame mutane 14,500.
Hamas tace dangane da fursunonin sahyoniyawa da Isra'ila ta kashe a hare-haren da ta kai Gaza: Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu ceci rayukan fursunonin Sojojin amma ta Isra'ila kashe su.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau cewa: Mun yi duk abin da za mu iya don ceto rayukan fursunonin amma Isara'ila ta kashe Sojojin na ta.
