20 Faburairu 2025 - 07:06
Gwagwarmaya Falasdinawa Na Shirin Miƙa Gawarwakin Fursunonin Isra'ila A Yau

Gwagwarmaya Falasdinawa Na Shirin Miƙa Gawarwakin Fursunonin Isra'ila A Yau Inda Ta Kafa Babbar Bana Da Ke Ɗauke Da Cewa Muddun Aka Ci Gaba Da Yaƙi Tom Gawarwakin Fursunonin Isra'ila Ne Kaɗai Zasu Koma Isra'ila

Kamfanin dillancin labaran Shahab ya wallafa wadannan hotunan gwagwarmayar Palasdinawa da ke shirya wajen mika gawarwakin wasu 'yan Isra'ila hudu a yankin Bani Suhaila da ke gabashin Khan Yunis a kudancin zirin Gaza.

Tawagar Falasdinawa ta sanya wata tuta a wurin miƙa wasu fursunonin Isra'ila hudu a Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, inda take ɗauke da cewa: Dawowar yaki na nufin komawar fursunonin Isra'ila a cikin akwatunan mutuwa.