15 Faburairu 2025 - 16:41
Bidiyon Yadda Hamas Ta Gudanar Da Taron Sakin Fursunonin Isra'ila 3 A Yau

Wannan rahoto yana dauke da bidiyo ɗaukar sama na yankin da taron sakin fursunonin Isra'ila 3 ya gudanar

Kamfanin dillancin labarai na Shahab ya buga faifan bidiyo ɗaukar sama na taron sakin fursunonin Isra'ila uku da dakarun Al-Qassam da Quds suka yi a Khan Yunis.

A Yau a cigaba da musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila An saki fursunonin Palasdinawa 369 a mamadin fursunonin sahyoniyawa 3

Bisa yarjejeniyar da akai a musayar kowane fursuna na Isra'ila, gwamnatin mamaya za ta saki fursunonin Palasdinawa 12 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai da kuma wasu fursunoni 111 daga Gaza da aka kama bayan 7 ga Oktoba, 2023.

A dunkule wannan mataki zai hada da sakin Falasdinawa 36 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai da kuma fursunoni 333 daga Gaza. Alkaluma sun nuna cewa wannan gungun ya kasance rukuni mafi girma na fursunonin Falasdinu da aka sako.

Wanda Har zuwa yanzu akwai fursunonin Isra'ila 73 a Gaza bayan waɗannan da aka sako yau.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta Yahudanci ta sanar da cewa bayan sakin fursunoni uku a Gaza a yau, har yanzu akwai sauran fursunonin Isra'ila 73 a Gaza.