Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta maku cewa: Nabih Berri, shugaban majalisar dokokin kasar Labanon, ya jaddada a ranar Alhamis cewa, ba za su bari sojojin yahudawan sahyoniya su ci gaba da zama a doron kasar ba. Wannan kuwa ya biyo bayan kawo ƙarshen wa'adin da aka bawa sojojin Isra'ila na kasancewa a ƙasar Labanon wanda zuwa yanzu suka ki ficewa daga ƙasar bisa goyon bayan ƙasar Amurka.
