Kamar yadda Kamfanin Dillancin
Labarai na Ahlulbaiti (ABNA) ya ta kawo maku cewa, an haifi Imamul Hujjah
(Allah Ya gaggauta bayyanarsa) a gidan mahaifinsa, Imam Hasan Al-Askari
(amincin Allah ya tabbata a gare shi) a birnin Samarra, a daren Juma'a, sha
biyar ga watan Sha'aban, wannan yana daga cikin darare masu albarka da aka
ambace su a cikin ranakun da akeson rayawa da ibada da azumtar ranekunsa tabbas
akwai riwayoyi masu inganci wacce aka ruwaito a ingantattun littafai kamar
Sunan Ibn Majah, Sunan Tirmidhi, da sauran littafan Sunna [1], ban da abin da
aka ruwaito daga Imaman Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) [2].
Shekarar da aka haife shi ita ce (255H) kamar yadda mafi shaharar ruwayoyi suka zo, akwai kuma wasu ruwayoyin da suka ambaci shekarar maulidinsa a (256H) ko kuma (254 AH) tare da ittafaki a ranar 15 din duk da wasu ruwayoyin sun ruwaito sabanin hakan, amma mafi kusantar ita ce ta riwayar farkon saboda wasu hujjoji da dama, ciki har da ambatonsa a cikin manya-manyan madogaran da suka rubuta labarin haihuwarsa, wanda shi ne littafin Gaiba na Shaikh Siqa Fadl dan Shazan wanda ya rayuwa a zamanin haihuwar Imam Mahadi (amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma ya rasu jim kadan kafin wafatin Imam Hasan Al-Askari (amincin Allah ya tabbata a gare su)[3], kuma daga cikinsu akwai cewa mafi yawan ruwayoyin sun yi nuni da cewa ranar haihuwar ta kasance ranar Juma’a ce a tsakiyar watan Sha’aban, duk da cewa sun yi sabani wajen bayyanar da shekarar da aka haife shi, kuma ta hanyar nazarin lissafin da mu ka yi mun samu cewa 15 ga watan Sha’aban ya dace da ranar juma’a ne a shekara ta (225h) wato wannna shekarar ita kadai koma bayan sauran shekarun da aka anbata a sauran ruwayoyin.
Irin wannan bambamci lamari ne na dabi’a da yake gudana a ranakun haihuwa da wafatin mahaifansa har ma da kakansa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ba tare da hakan ya shafi hujjar haihuwarsu (amincin Allah ya tabbata a gare su) ba, kuma yana da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da sirrin haihuwarsa a lokacin da ya faru domin kiyaye jaririn mai albarka.
Ruwayoyin haihuwa mai albarka (amincin Allah ya tabbata a gare shi sun kai haddin Tawaturi: wanda Malamai da yawa sun ruwaito kissa ko labarin haihuwar da sanadodi ingantattu kamar irinsu: Abu Ja’afar Dabari da Fadal dan Shazan da Husain dan Hamdan da Ali dan Husain Al’Mas’udi da Shaikh Saduk da Shikh Dusi da Shaikh Mufid da sauransu. Kuma malaman Ahulus Sunna dayawa daga mabanbantun mazhabobi na musulunci, kamar irinsu Shaikh Nuruddin Abdurrahman Aljami Alhanafi a littafinsa Shawahdun NUbuwwa, da Allamah Muhammad Mubin Almaulawi Alhindi a littafinsa Wasilatun Najat, da Allamah Muhammad Khawajah Barsa Albukhari a littafin Faslul Khidab da Hafiz Sulaiman Al-Qanduzi a Yanabi’il Mawaddah. Haka nan kuma kusan malamai dari da talatin ne daga mazhabobi daban-daban na Musulunci suka kawo labarin, wadanda suka hada da gomman masana tarihi, wadanda shida daga cikinsu sun yi rayuwa a lokacin Gaiba karama ko kuma a lokacin haihuwar Imam Mahdi (amincin Allah ya tabbata a gare shi), sauran kuma tun daga karnoni daban-daban har zuwa yau a cikin tsawon shekaru, wannan kidayar ta hada da wani kaso daga cikin madogaran Musulunci ne kawai ba duka ba. Daga cikinsu akwai ɗimbin mashahuran malamai da masana tarihi, irin su Ibn Khillikan, Ibn Athir, Abul-Fida, Az zahabi, Ibn Tulun Dimashqi, Sibt Ibnul Jawzi, Muhyid Din Ibn Arabi, Al-Khwarizmi, Baihaqi, Safadi, Yafi’i, Karmani, Ibn Hajaril Haisami, da sauransu. Wanda Irin wannan hujja ba ta samuwa ga haihuwar fitattun mutane da yawa a tarihin Musulunci[5].
Yanayin Haihuwarsa:
An fahimta daga ruwayoyi game da yadda aka haife shi (amincin Allah ya tabbata a gare shi), cewa mahaifinsa Imam Hasan Askari (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya lullube lamarin haihuwarsa, Ruwayoyin sun an ambaci cewa Imam Hasan Al-Askari ya ce wa Yar uwarsa, Sayyidah Hakima, ‘yar Imamul Jawad As, da ta zauna a gidansa a daren Sha’aban. Kuma ya bata labarin cewa a daren ne za a haifi dansa kuma hujjar Allah a dodron kasarsa, sai ta tambaye shi game da mahaifiyarsa, sai ya ce mata ita ce Narjis, sai ta je wurinta, ta duba ta, amma ba ta samu wani alamar ciki ba, sai ta koma wajen Imam, ta ba shi labari, sai ya yi murmushi, ya bayyana mata cewa, ta kasance kamar mahaifiyar Musa (as) wacce cikinta bai bayyana ba kuma babu wanda yasan za ta haihu har lokacin da ta haife shi domin Fir’auna yana bibiyar haihuwar ‘yayan bani Israila domin yana jin tsoron bayyanar Musa, wanda aka yi masa alkawari da zuwansa, sai ya rinka yanka ‘ya’yansu maza, ya na barin matansu, shi ma haka wannan lamarin ya faru da Imam Mahdi (As).
Imam Mahdi (Allah Ya Gaggauta Bayyanarsa) A Cikin Alkur'ani Mai Girma
Alkur'ani mai girma ya ambaci ayoyi da dama da suke nuni da bayyanar Imam Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanar da shi) kuma sun zo a cikin ingantattun ruwayoyi domin kuwa lamarin baiyanar Imamin da ake jira (Allah Ya gaggauta bayyanar da shi) yana da matukar muhimmanci wajen gyara tushen addinin Musulunci kuma kamar yadda bushara ta zo acikin littafan addinan da suka gabaci addanin Musulunci wacce kuma ya kasance tana da muhimmanci matuka a kasancewarta a cikin ayoyi Kur’ani mai girma. A nan kasa zamu ambaci wasu ayoyi da suka yi nuni da bushara ga mutanen zamanin da za a kawar da zalunci a cikinsa kuma za a raya adalcin Ubangiji daga cikin wadannan ayoyi akwai:
Na farko: Fadinsa Madaukaki: {Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun rubuta a cikin Zabura, a bãyan Zikir, cẽwa bãyina salihai ne zasu gaje ƙasa} (6).
أولا:- قوله تعالى: {وَلَقَدْ كَتَبْنَا فِي الزَّبُورِ مِنْ بَعْدِ الذِّكْرِ أَنَّ الْأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ الصَّالِحُونَ}(6).
Sheikh Al-Tabarsi, Allah Ta’ala Ya yi masa rahama, ya ce a cikin tafsirinsa na ayar: { {أَنَّ الْأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ الصَّالِحُونَ} bayina salihai ne za su gaji kasa} Abu Ja’afar, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Su ne sahabban Imamul Mahadi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a karshen zamani.
Wannan yana nuni da abin da Amma da Khassa suka riwaito daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ke cewa: “Da a ce duniya za ta kasance saura kwana daya, da Allah ya tsawaita wannan ranar har sai Ya aiko da wani mutum mai adalci daga iyalina, wanda zai cika kasa da adalci da daidaito, kamar yadda ta cika da zalunci (7).
Na biyu: FadinSa Madaukaki: {(Shi ne wanda ya aiko Manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya bayyana shi a kan dukkan addini, ko da kuwa wadanda suka yi shirka da Allah ba su son hakn) (8).
ثانيا :- قوله تعالى: {هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدَى وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ}(8).
Al-Shaykh Saduq ya ruwaito daga Abu Basir ya ce: “Abu Abdullah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce dangane da fadin Allah Ta’ala: {هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدَى وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ}, ya ce: “Wallahi ba a saukar da ta’awilinta ba, kuma ba ta’awilinta ba zai kasance sai, sai Qaim ya bayyana a kansa, idan ya bayyana, babu wani mai kafirci ga Allah Madaukakin Sarki, ko mushriki da zayyi saura fa ce yayi kiyayya da bayyanarsa ko da akwai kafiri ko mushriki a cikin cikin dutse sai dutsen ya ce: Ya kai Mumini, cikin cikina akwai kafiri, sai ka karya ni ka kashe shi (9).
Na uku: Allah Ta’ala yana cewa: {Allah ya yi wa wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na qwarai daga cikinku alkawari,, cewa lalle ne zai sanya su magada a bayan qasa, kamar yadda ya sanya waxanda suka gabace su su maye gurbinsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda ya yarje ma su, kuma lalle ne zai musanya musu da aminci, bayan tsoronsu [alhali] suna masu bauta mini, ba sa shirki da Ni(10).
ثالثا:-قوله تعالى:{وَعَدَ الله الَّذِينَ آَمَنُوا مِنْكُمْ وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِي الْأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضَى لَهُمْ وَلَيُبَدِّلَنَّهُمْ مِنْ بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْنًا يَعْبُدُونَنِي لَا يُشْرِكُونَ بِي شَيْئًا}(10).
Furat Al-Kufi ya ruwaito cewa: An karbo daga Suddi, daga Ibn Abbas, Allah Ya yarda da shi, dangane da fadinsa Madaukaki: {(Allah Ya yi wa wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai daga cikinku alkawarin cewa zai sanya su magada a bayan kasa}) har zuwa karshen ayar, ya ce: An saukar da ita ne akan alayen Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa (11).
Wadannan wasu misalan ne, kuma akwai ayoyi da yawa da ba za a iya kunsa su a cikin wannan taqaitaccen rubutun ba (12). Amma wasu suna mamakin me ya sa ba a ambaci sunan Imam da ake jira ba ko kuma batun fakuwar Imam da zamanin bayyanarsa a cikin Alkur'ani mai girma? Amsa ita ce: Alkur’ani mai girma bai fadi wasu abubuwa da yawa dalla-dalla ba, sai dai duk bayanan da suka shafi wadannan lamurra sun samo asali ne daga ruwayoyin da aka ruwaito daga Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su). Kamar yadda Allah Ta’ala ya anbaci sallar wajibi amma bai anbaci adadin raka’oinsu ba acikinsa sai dai ya bar hakan a riwyoyin da suke fassara wadannan hukumomin da mas’alolin na shari’a……
Madogara:
__________________
[1] Duba, misali, Musnad Ahmad bn Hanbal: 2/176, Sunan Ibn Majah: 1/444-445, Fayd al-Qadir: 4/459, Sunan al-Tirmidhi: 3/116, Kanzul-Ummal: 3/466, da dai sauransu.
[2] Sawabul A’amal na Sheikh Saduq: 101, Misbahul mUtahajjid na Sheikh Al-Tusi: 762, Iqbalil A’amal na Sayyid Ibn Tawus: 718.
[3] Duba wadannan ruwayoyin a cikin littafin An-Najmus-Thaqib na Mirza Al-Nuri: 2/146 da abin da ya biyo baya a fassarar larabci, sai a duba Al-Kafi: 1/329, Kamalud Din: 430.
[4] A aikace muna nufin kalandar da ake tsakanin ranakun kalandar Shamsiyya da kwanakin kalandar Qamriyya da suka yi daidai da su, an shirya kalandar da yawa irin wannan a cikin nau'i na littattafai ko shirye-shiryen kwamfuta waɗanda suka tabbatar da abin da kowace rana ta Hijiriyya Shamsiyya da ta yi daidai da kalandar ranar Hijiriyya Qamriyya da kuma shekarar miladiyya Shamsiyya. Kuma mun bibiyi wanna binciki ne a kalandar da Jami’ar Tehran wacce ta fara daga shekarar farko ta hijirar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam) har zuwa karshen karni na sha biyar Hijira.
[5] Duba dalla-dallan maganganunsu a kididdigar da Sayyid Samir Al-Amadi ya bayar a cikin littafinsa mai suna "Difa’u ANil-Kafi": 1/535-592.
[6]_ Suratul Anbiya, aya ta: 5.
[7]_ Tafsirin Majmaul-Bayan, Sheikh al-Tabarsi: 7/120.
[8] Suratul Taubah, aya ta: 33.
[9]_ 5- Kamalud Deen Wa Tamamun Ni’imah, Sheikh Saduq: 670 H16, Tafsirin Furat Al-Kufi: 481-482 H3.
[10] Suratul Nur, aya ta: 55.
[11]_ Tafsirin Furat Al-Kufi: 288-289 H3 da H6.
[12] Duba littafin “Mahdiyul Umam (Af)” (na Abdullah Al-Hassan), shafi na 332.
