Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Ƙungiyar Hamas tayi bayanin kan zaman da sukai da kuma kaiwa da komowa na cigaban yarjejeniyar musayar fursunonin in da ta ce: Muna jaddada ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar, gami da musayar fursunoni bisa a lokacin da aka amince.
Kuma Mun tattauna da masu shiga tsakani domin tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni, musamman bayan da gwamnatin mamaya ta karya yarjejeniyar farko.
Tawagarmu da ke birnin Alkahira ta gana da shugaban hukumar leken asiri ta Masar, inda kuma ta tattauna ta wayar tarho da firaministan Qatar, kuma ta gana da masu gudanar da shawarwarin a Masar da Qatar, da kuma tawagar kwararru.
Wadannan kiraye-kirayen da tarurrukan sun mayar da hankali ne kan aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar, musamman wadanda suka shafi samar da gidaje ga al'ummarmu da kuma kai Tantuna cikin gaggawa.
Wadannan kiraye-kirayen sun kuma mayar da hankali kan samar da tantuna, manyan kayan aiki, kayayyakin jinya, man fetur, da kuma ci gaba da jigilar isar da kayan agaji.
