Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) – ABNA – ya habarta maku cewa: Duk da kasancewar dubban 'yan gudun hijirar Palasdinawa tare da ayyana cewa ba za a kai wa al-Mawasi hari daga gwamnatin sahyoniyar ba, amma yan mamayar sun kai hari a wannan yanki da bama-bamai "MK-84" guda uku.
Wannan bam yana da nauyin kilogiram 907, yana dauke da bama-bamai kimanin kilogiram 400, kuma gudun kadawarsa da yake fitarwa a halin yanzu yana da karfin gaske.
Fashewar wannan bam yana haifar da hujewa da tare da yin kofofi a jikin hunhu da kakkarye gabban jiki da fashewar kawukan sinus sannan kuma matsanancin takurarar da yake sanyawa yana iya ruguza gine-gine kuma munanan cutar da yake watsawa tana ci gaba da yin nisan mita 350.
Duk da wannan barna, Isra'ila na
ci gaba da amfani da wadannan bama-bamai a wuraren da jama'a ke da yawa. Ana
amfani da wannan bam ne yayin da yahudawan sahyoniya suke da bama-bamai da aka
tsara don rage asarar fararen hula.
Abin da ke faruwa a arewacin zirin Gaza bai faru a wani wuri a duniya ba
Ismail Thawabateh, darektan ofishin yada labarai na hukumar Falasdinu a Gaza, a wata tattaunawa da yayi da tashar Aljazeera:
Gwamnatin mamaya bisa tsari tana aiwatar da hadafin kakaba yunwa a kan al'ummar Palasdinu a zirin Gaza, musamman ma mutane masu rauni.
"Yawan abincin da ke kaiwa mutanenmu bai kai kashi 5% na ainihin bukatunsu ba."
Yunwa ta lalata iyalai da ke sansanin Jabalia gaba daya, kuma yanayin jin kai yana da muni.
Ya kamata kasashen duniya su gaggauta bude hanyoyin shigar da abinci da na jarirai da kuma hana afkuwar bala'in rashin jin kai.
"Abin da ke faruwa a arewacin zirin Gaza bai taba faruwa a wai wuri a duniya ba kuma ga wata kasa a tarihi."
Asibitocin Kamal Adwan, Al-Awda da Indonesiya na gab da dakatar da ayyukansu saboda rashin kayan aiki da kayan aikin jinya.
Da yake sukar ayyukan kungiyoyin kasa da kasa, Sawabata ya fayyace cewa wadannan kungiyoyi sun kasa bayar da mafi karancin tallafi ga al'ummar Palasdinu, kuma ba su dauki kwararan matakai na dakile laifukan gwamnatin mamaya ba.