A cikin sanarwar da sojojin suka
fitar, wadannan bataliyoyin sun sanar da cewa, cikin matukar alfahari da imani
da samun nasarar Allah a nan kusa, sun shelanta shahadar wasu gungun manyan ‘ya’yanta,
wato Shahidi Dosum Sufyan Al-Aufi, Shahid Muhammad Isa Al-Aufi da Shahid Muhammad
Nafiz Raheima.
Qassam ta jaddada cewa wadannan manya-manyan mujahidan tare da takwarorinsu shahidi Mujahid Tariq Mahmoud Al-Dosh, sun samu shahada ne bayan wani mummunan hari ta sama da dakarun yahudawan sahyoniya suka kai kan motarsu da ke sansanin Tulkarm da ke arewacin yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye.
Bataliya ta Qassam ta jaddada cewa yayin da suke bankwana da wadannan Mujahidan, sun sake sabunta yarjejeniyarsu da Allah da al'ummar Palastinu da al'ummar musulmi domin daukar fansa kan jinin shahidan da suka sadaukar da rayukansu ga addini da kasa mai tsarki ta Falasdinu.