Mun kasance a shirye a cikin
wannan mawuyacin hali. Suka zo nan, suka ce mini, mun shirya dukkan kayayyakin
da ake bukata ga mutanen Sham a yau, kuma a shirye muke mu tafi, [amma] an rufe
sararin sama, an rufe kasa; Gwamnatin Sahayoniya da Amurka sun rufe dukkan
sararin samaniyar Siriya da hanyoyin kasa; Bai yiwu ba mu kai dauki ba. Abubuwa
sun kasance haka. Idan a cikin wannan kasa, idan ya zamo ako wani yunkuri da
buri da yayi saura to zasu iya gaba da gaba da abokan gaba, kuma makiya ba za
su iya rufe sararin samaniyarsy ba, kuma ba za su iya rufe hanyar kasa ba; to
da ana iya taimaka musu. To, wannan shine yadda abun yak e a dunkule.
Akwai 'yan ƙarin batutuwa da zan faɗa. Batu na farko shi ne, kowa ya sani cewa matsalar ba za ta tsaya haka ba; Idan wata kungiya ta zo Damascus ko wasu wurare, ta yi murna, ta yi raye-raye, ta mamaye gidajen mutane, gwamnatin Sahayoniya ta zo ta jefa bama-bamai, ta kawo tankokin yaki, ta kawo igwa, lamarin ba zai wanzu a haka ba; Babu shakka matasan Siriya masu kishi za su tashi tsaye, za su tsayindaka, za su yi sadaukarwa, su ma za su sha wahala, amma za su shawo kan wannan lamarin. Kamar yadda matasan Iraqi masu kishi suka yi haka; Matasa masu kishi na kasar Iraki tare da taimako da jagoranci da nusatanwar bisa tsari na shahidin mu masoyinmu sun sami nasarar fatattakar makiya daga lunguna da tituna da fitar da su daga gidajensu, domin irin haka Amurkawa suke yi Iraki. Suna fasa kofar gidajen, su sanya mai gidan ya kwanta a gaban matarsa da yaransa, suna danne fuskarsa a kasa da takalminsu! Haka nan a kasar Iraki ma haka ta faru, amma sai suka tsaya tsayin daka suka yi gwagwarmaya, shi ma shahidinmu ma ya bayar da dukkan abin da ya dace. Haka za su yi. Tabbas, yana iya ɗaukar lokaci, yana iya zama tsayi, amma sakamakon tabbatacce ne.
Abu na biyu shi ne cewa lamarin Siriya yana dauke da darasi, darasi a gare mu - ga kowannenmu, ga jami'anmu; Dole ne mu koyin darasin. Daya daga cikin darussa wannan mas’alar ita ce “gafala sakaci”; yin sakaci da makiya. Haka ne, a cikin wannan lamari, makiya sun yi sauri wajen gudanar da matakin, amma kafin faruwar lamarin ya kamata su sani cewa wannan makiya za su yi gaggawar daukar mataki. Mu ma mun taimake su; ma’aikatar bayanan sirrinmu mu ta aike da rahotanni gargadi ga hukumomin Syria a 'yan watannin da suka gabata. Tabbas, ban sani ba shin wadannan [rahotanni] sun kai ga wadancan manyan jami’an ne ko a’a, ko sun bata ne a tsakani; Amma jami’an bayananmu mu sun shaida musu. Tun daga yaushe Sun tunatar da su tun daga watan Shahrivar, Mehr, Aban, akai akai. Kada kuyi sakaci, kada ku yi sakaci da makiya; Kada a raina makiya, kuma kada a amince da murmushin makiya; Wani lokaci maƙiyi yana magana da mutane cikin sauti mai daɗi, yana magana da murmushi, amma yana riƙe da wuƙa a bayansa yana jiran dama.
Wani batu na gaba kuma shi ne, bai kamata fagen gwagwarmaya bai kamata yayi alfahari da samun nasara ba, kuma bai kamata ya yanke tsammani don ya sha kayi ba. Akwai nasara da rashin nasara a koyaushe suna zuwa. Rayuwar mutane hakan ta ke: a cikinta akwai nasara, akwai rashin nasara; haka Rayuwar kungiyoyi ma take: a cikinta akwai nasara, akwai gazawa. Wata rana yana gudanar aikinsa, wata rana ya zamo an sauke shi daga kan aiki; suma Gwamnatoci haka abun ya ke, suma kasashe hakane. Akwai kwari da kwazazzabo a rayuwa; ’Yan Adam ba za su iya guje wa tashi da faɗuwa ba. Abin da ya wajaba shi ne kada mu yi alfahari yayin da muke yi sama; Domin girman kai yana kawo jahilci kuma girman kai yana sa mutane su yi sakaci. Lokacin da muka sauka kuma, muka gaza a wani wuri, bai kamata mu kasance cikin baƙin ciki da yanke tsammani da karayar zuciya ba.
A cikin wadannan shekaru arba'in, Jamhuriyar Musulunci ta fuskanci al'amura masu girma da wahala; Manyan al'amura! Matasan ba su ga wannan ranar ba; A cikin wannan Tehran din, mutanen Tehran suna zaune a gidajensu, jirgin yaki na MiG-25 na Tarayyar Soviet ta hannun Saddam, suna zuwa nan suna shawagi a sama da mu, idan yana da karamci, ba zai yi ruwan bamabamai ba, amma yana bayarda tsoro; Amma suna bayarda tsoro! Mu ma ba mu iya yin komai; Ba mu da kariyarsa, ba mu da kayan aikinsa. Amma mun yi gaba da gaba da su. Watarana a wannan birnin Tehran kowa na zaune a gidansu, jiragen saman Saddam kaitsaye sun zo nan suka jefa bama bamai a Tehran. Sun jefa bama-bamai a filin jirgin, sun jefa bama-bamai a wasu wurare. Ni da kaina na yi jawabi a wannan rana a wata masana'anta kusa da filin jirgin saman Tehran. Sai hayaniya ta tashi, muka tashi muka leka ta taga, ni da kaina na ga jirgin Iraqi ya sauko, ya jefa bama-bamai a filin jirgin ya tafi. Mun ga wadannan. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fuskanci wadannan lamurra daban-daban, al'amura masu daci, sai dai ba wani rauni a cikin wadannan lamurra na dan lokaci ba.