Qasim Salman al-Abudi ya jaddada
a cikin wata makala cewa: Ficewar fagen daga Siriya daga gwagwarmaya ba za ta
hana wannan gwagwarmaya ci gaba da gudanar da sahihin aikinta na tallafawa
al'ummar Palastinu ba da kowane dalili.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: bayan kifar da gwamnatin Bashar Assad a kasar Siriya, kungiyoyin siyasa da kafofin yada labarai na yankin da ma duniya baki daya, abokai da makiya masu adawa, sun yi magana game da batun muhimmin barakar da aka samu a cikin fagen gwagwarmaya. Sai dai tsarin gwagwarmaya da kuma shugabancinta bisa jagorancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya nuna cewa ta samu muhimman damammaki daga wanna barakar. Shahidi Sardar Sulaimani ya ce yayin jawabinsa; "Yawancin damar da ake samu a cikin rikice-rikice ba a cikin tabarbarewar da kanta ba ne, muddin ba mu ji tsoro ba, ba kuma mu tsoratar".
Dangane da haka wani masani dan kasar Iraqi "Qasim Salman Al-Abudi" ya rubuta makala ta musamman ga kamfanin dillancin labarai na Abna, wanda aka fassara rubutun zuwa harshen Hausa kamar haka:
A mahangar akida da addini ba Siriya ba ta taba nutsewa da shan kayi ba a tarihin gwagwarmaya, akidar da aka rayata a tafarkin gwagwarmaya bisa wajibcin shari'a da ta samu ci gaba akan tafarkinta tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran a shekarar 1979 karkashin jagorancin Imam Khumaini (RA) har zuwa 2011. Bayan wannan kwanan wata, tare da kokarin Haj Qasim Sulaimani, daidaiton siyasa a Damascus ya canza saboda dalilai da yawa. Babban abin da ya fi daukar hankali shi ne fargabar kasancewar kungiyoyi masu dauke da makamai a kusa da birnin Damascus, kungiyoyin da kasashen yankin tekun Fasha ke samar masu da kudaden tallafin da suke kokarin ruguza gwamnatin Bashar Assad a Siriya.
Bayan isowar gwagwarmayar matasa masu ra'ayin mazan jiya a Siriya da kuma sake fasalin gwamnatin Siriya tare da taimakon Rasha, shugaba Bashar ya fahimci babban hatsarin da ke fuskantar karagar mulkinsa. Ba zai iya amfani da tsarin gwamnatinsa ba wajen kare gwagwarmaya a yankin ba. To sai dai kasashe da gwamnatocin yankin irinsu Turkiyya, Isra'ila da kuma yammacin duniya ba su taba yin sakaci da kasar Siriya ba, saboda muhimmin matsayin da take da shi a yankin a daya bangaren da kuma hadin gwiwar da take da shi na gwagwarmaya a daya bangaren.
A lokacin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta gaza wajen yakar al'ummar Palastinu a Gaza, wannan gwamnatin ta tafi arewacin kasar Palastinu domin bude wani sabon fage da kungiyar Hizbullah a kudancin kasar Lebanon. Bayan gazawar sojojin yahudawan sahyoniya wajen yakar kungiyar Hizbullah, kasashen yammacin duniya sun baiwa Netanyahu koren haske ta hannun sojojin hayarsu wajen wuce zagaye gwagwarmaya tare da yi mata kawanya ta hanyar kifar da gwamnatin Asad.
Don haka bangarorin da suke cin gajiyar wannan lamari kamar gwamnatin Sahayoniya da Turkiyya da kasashen Larabawa na Tekun Fasha bisa umarnin babbar shaidan Amurka sun shiga shirin kifar da gwamnatin Bashar Assad kuma wannan faduwa ce mai muni.
Batun ya samo asali ne daga sakamakon yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, wani dalili ne da ya sa Rasha ta tsoma baki a yunkurin hambarar da gwamnatin Bashar ta hanyar ba da lamuni daga kasashen yamma na dakatar da zubar da jinin da ake yi a Rasha, tare da sharadin cewa idan Moscow ta amince da shawarar kasashen yamma, Yamma za su yanke goyon bayan da suke yi ga Ukraine. Don haka an kulla wannan yarjejeniya a daya daga cikin manyan biranen kasashen Larabawa da ke gabar tekun Farisa tare da halartar kasar Rasha.
A yau fagen gwagwarmaya ya rasa daya daga cikin muhimman bangarorinsa wajen fuskantar girman kai na sahyoniyawa. An shirya wannan shiri ne a hanyoyin leken asiri na Amurka, Ingila, Turkiyya, Isra'ila da Qatar kafin matakin tsagaita bude wuta tsakanin Hizbullah da gwamnatin sahyoniyawa.
Tehran ta hannun jami'anta ta samu shedu dangane da wannan batu, ta kuma sanar da Bashar Assad aniyar kasashen yammacin duniya na hambarar da shi, amma Assad bai yarda ba. Da gangan ya tursasa wasu jagororin gwagwarmaya da ke zaune a Siriya. Saudiyya ta yi wa Assad alkawarin cewa Syria za ta koma hannun Larabawa da zarar ta janye goyon bayanta ga kungiyar Hizbullah tare da sarrafa ikonta akan ofishin jakadancin Yemen a Damascus. Ya bi wadannan umarni har ma ya kori wasu mashawartan sojojin Iran daga Siriya. Ya yi imanin cewa kasashen yamma za su gamsu da shi ta wannan hanya kuma Rasha za ta goyi bayansa a duk wannan hanya.
A yau, gwagwarmaya za ta sami wani wanda zai maye gurbinta bayan tafiyar Assad. Wannan akidar ba za ta iya amincewa da kungiyoyin da ke dauke da makamai na Syria ba, ta yadda kowace kungiyar ta dogara da wata jam’iyyar waje. Janyewar da Siriya ta yi daga kan turbar gwagwarmaya ba zai hana wannan fage ci gaba da halaccin aikinta na tallafawa al'ummar Palastinu da kowane dalili.
Mun yi imanin cewa, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon za ta dauki wasu zabin, wadanda a baya da ta dogara da Syria wajen samun makamai da kera makamai.
A yau, bayan rugujewar gwamnatin Bashar Assad, dole ne a samar da wata hanyar da za ta tallafa wa bangaren Lebanon ta hanyoyin da ba na kofar Damascus ba. Na'am, tafiyar Assad ta yi tasiri a kan kusurwoyin gwagwarmaya, amma wannan akidar ba za ta taba rasa ruhin tsayin daka ba, kuma a cikin kwanaki masu zuwa, igiyar gwagwarmaya za ta sanar da mu dabarun nasarar da ta samu wajen neman wani sabon madogarar madadin Syria.
Don haka muna da cikakken imani cewa gwagwarmayar Musulunci tana ci gaba kuma ba zata gushe ba saboda albarkar shugabanta Imam Hujjah bin Hasan (a.s).