Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta bisa nakaltowa daga tashar watsa labaran -IRNA- cewa: Majiyoyin labarai sun sanar da cewa gwamnatin yahudawan sahyuniya ta sake karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Labanon.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta hakan bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na tashar Al-Mayadeen cewa, gwamnatin sahyoniyawan ta kai hari kan yankin "Haris" da ke kudancin kasar Lebanon a wani harin da jiragen yaki mara matuki, kuma a wannan harin 'yan kasar Lebanon 6 ne suka yi shahada ciki har da mace daya da wani karamin yaro.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon ta tabbatar da labarin shahadar 'yan kasar 6 tare da sanar da jikkata wasu guda 2.
A daren jiya litinin ma gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai hare-hare a kudancin kasar Lebanon.
A cikin hare-haren ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ili ke yi a yammacin jiya litinin 'yan kasar Lebanon 9 ne suka yi shahada tare da jikkata wasu uku a hare-hare biyu da wannan gwamnatin ta kai kan garuruwan Haris da Taluseh. A sa'i daya kuma, Isra'ila ta kai hari kan garuruwan kudancin kasar Lebanon, sannan jiragen yakinta suna ta yin shawagi a sama kasa-kasa a Beirut da Dahiya.
A gefe guda kuma, a jiya litinin, kungiyar Hizbullah ta mayar da martani kan karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra'ila ta yi a karon farko tun bayan kafuwar yarjejeniyar, kuma a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce matakin gargadin farko ne tare da kai hari kan tsakiyar sojojin gwamnatin mamaya a yankunan da ta mamaye na Kafr Shoba
A safiyar Laraba 27 ga watan Nuwamba ne yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin gwamnatin Sahayoniya da Lebanon tare da shiga tsakani na kasa da kasa ta fara aiki.
Tun bayan aiwatar da wannan yarjejeniya, sojojin Isra'ila sun sha keta ta tare da hana 'yan gudun hijirar Lebanon komawa wasu garuruwa da kauyukan kudancin wannan kasar.
Shugaban majalisar dokokin Lebanon Nabih Berri ya sanar a ranar Litinin cewa: Adadin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra'ila ta yi ya zarce 52.
Ana haka kuma tashar Al Jazeera ta ruwaito cewa: Tawagar sa ido kan tsagaita bude wuta ta isa Lebanon
Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, tawagar da ke sa ido kan tsagaita bude wuta na kasa da kasa a kasar Lebanon ta fara aikinta, kuma jami'an Lebanon da na sahyoniyawa sun dake kan cewa sun amince da tsagaita bude wuta.
A cewar rahoton da IRNA ta fitar a yau Talata, kafar yada labarai ta Aljazeera ta nakalto majiyar Amurkawa, ta sanar da cewa tawagar da ke sa ido kan tsagaita bude wuta ta isa kasar Lebanon domin fara aikinta.
Wadannan majiyoyin sun jaddada cewa Washington tare da Faransa da Lebanon da kuma gwamnatin sahyoniyawan suna kokarin warware dukkan batutuwan da suka shafi tsagaita wuta.
Majiyoyin Amurka sun ce Washington za ta yi iya kokarinta wajen ganin an tsagaita bude wuta kuma ta yi imanin cewa za ta dore.
Wadannan majiyoyin sun kara da cewa: Washington na tattaunawa sosai da jami'an Lebanon da na Isra'ila dangane da tsagaita bude wuta. Jami'an bangarorin biyu sun sha nanata yadda suke bin wannan tsagaita bude wuta.
An buga wannan labarin ne yayin da gwamnatin Isra'ila ta kai hare-hare a kudancin Lebanon a daidai lokacin da take ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a daren Litinin.