Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: A cewar Al-Manar, mutane da dama ne suka jikkata sakamakon sabon harin da Isra'ila ta kai kan wani gini da ke garin Deir Qanun al-Nahar a kudancin kasar Lebanon.
Ita ma tashar talabijin ta Aljazeera ta fitar da cewa sojojin Isra'ila sun sanar a yau cewa, a hari na hudu da aka kai a Dahiyatu birnin Beirut, sun kai hari ne kan ma'ajiyar makamai da kayayyakin more rayuwa na kungiyar Hizbullah.
Shima Kamfanin dillancin labaran Sama ya habarta cewa, gwamnan lardin Baalbek da Al Harmel ya bayyana cewa: Bisa kididdigar da aka yi na farko, mutane 47 ne suka yi shahada yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan biranen lardin Gabashin kasar Lebanon.