21 Nuwamba 2024 - 18:19
Martanin Netanyahu Kan Sammacen Kama Shi Da Kotun Manyan Laifuka Bayar

Netanyahu ya fusata kan sammacin kama shi

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: Firaministan Isra'ila Netanyahu, a martanin da ya mayar kan sammacin kama shi da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yi, ya bayyana wannan kotu a matsayin ta "siyasa" kuma ya siffanta mai gabatar da kara na kotun a matsayin "mai cin hanci da rashawa".