21 Nuwamba 2024 - 15:49
Hague Ta Bayar Da Sammacin Kame Netanyahu Da Gallant Bisa Zargin Aikata Laifukan Yaƙi A Gaza

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kama Benjamin Netanyahu da Yoav Galant.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta bisa nakaltowa daga tashar sadarwa ta Aljazeera cewa: Wannan kotun ta bayyana cewa akwai dalilai masu ma'ana da za mu yarda da cewa Netanyahu da Gallant sun aikata laifin yaƙi.

Biyo bayan wannan furici ana samu martanoni daga ɓangaren biyu da ke kishiyantar juna bisa wannan hukunci na wannan kotun koli martanin farko da ke nuna gamsuwa da wannan hukuncin ya fito ne daga ɓangaren Kungiyar Hamas inda ta yi maraba da hukuncin da kotun Hague ta yanke kan Netanyahu

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta yi maraba da sammacin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague ta bayar ga Benjamin Netanyahu da Yoav Galant, firaministan kuma tsohon ministan yakin gwamnatin sahyoniyawa 'yan ta'adda, bisa zargin aikata kisan kiyashi da kuma aikata laifukan yaki akan 'yan Adam a Gaza, kuma taa bukaci a gaggauta hukunta masu laifin yakin na sahyoniya.

A bangare guda kuma ɓangaren 

Trump in da ya nuna goyon bayansa ƙarara ga masu aikata laifukan ta'addanci na duniya da cewa: Kotun hukunta laifuka ta duniya ba ta da wani anfani!

Mai baiwa zababben shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Donald Trump ya sanar a wata sanarwa mai cike da cece-kuce cewa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ba ta da wani sahihanci kuma ba za ta iya ikirarin halaccinta ba.

Ya jaddada cewa Amurka ba ta da wani nauyi a wuyan wannan kotu saboda damuwar da ke da alaka da ikon mallakar kasa da kuma yiwuwar cin zarafi. Wadannan kalamai wani bangare ne na matsayin da gwamnatocin jamhuriyar Amurka suka saba dauka game da cibiyoyin kasa da kasa, wadanda galibin hakan martanoni da dama sun biyo daga kasashen duniya.