21 Nuwamba 2024 - 08:08
Isra'ila Ta Sake Aikata Wani Sabon Kisan Kiyashi A Gazza.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da safiyar Alhamis din nan cewa akalla Falasdinawa 60 ne suka mutu kana wasu 100 suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai a wata unguwa da ke kusa da asibitin Kamal Udwan da ke arewacin zirin Gaza.

Wani sabon kisan kiyashi a arewacin Gaza tare da shahidai 160 da jikkata

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da safiyar Alhamis din nan cewa akalla Falasdinawa 60 ne suka mutu kana wasu 100 suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai a wata unguwa da ke kusa da asibitin Kamal Udwan da ke arewacin zirin Gaza.

Jami'in UNRWA: Gaza Ta Zama Maƙabartar Yara

Lazzarini, Babban Kwamishinan Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka na Majalisar Dinkin Duniya UNRWA, ya bayyana cewa, a yau shekaru 30 bayan amincewa da Yarjejeniyar 'Yancin Yara, muna shaida cewa ana bin take hakkin yaran Falasdinawa da keta hakkinsu a kowace rana, musamman ma yankin Gaza da ya zama makabartar yara.

A daidai lokacin da ake bikin ranar yara ta duniya, an gudanar da zaman makoki ga yaran Gaza da ake zalunta

Kimanin watanni 14 kenan 'yan sahayoniya suke kashe kananan yaran Palastinawa, kuma da yawa daga cikinsu da suka tsira sun rasa iyalansu sun zamo su kadai.

Kimanin yara 17,500 ne suka yi shahada a yakin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi da zirin Gaza.

211 daga cikin shahidan jarirai ne da aka haifa a lokacin yakin.