Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta maku cewa, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar da sanarwa tare da sanar da cewa Mohammad Afif Al-Nabulsi jami'in yada labaran kungiyar Hizbullah ya yi shahada a yayin harin zaluncin da yahudawan sahyuniya suka yi a baya-bayan nan.
Ga bayanin bayanin kamar haka:
Shahadar fitaccen dan jarida kuma shahidin tafarkin mai tsarki Haj Muhammad Afif Al Nabulsi mai kula da harkar huldar yada labarai na kungiyar Hizbullah, bayan harin ta'addancin gwamnatin sahyoniyawa, bayan ya dauki tsawon lokaci yana aiki a tafarki mai daraja a fagagen jihadi da ayyukan watsa labarai na fagen gwagwarmaya da jihadi ga al'ummar gwagwamaya da kafafen yada labarai na gwagwarmaya da al'ummar shahidai da mayaka Muna mika ta'aziyyarmu.
Kungiyar Hizbullah ta jaddada ci gaba da tafarkin shahidan tana mai cewa ba za a taba mantawa da tunawa da shahidan ba, kuma makiya yahudawan sahyoniya za su biya babban farshin na laifukan da suka aikata.