14 Nuwamba 2024 - 13:43
Ikrarin Yahudawan Sahyuniya Ga Karfin Makami Mai Linzami Na Hizbullah Da Kuma Rashin Amfanin Ayyukan Sojin Akan Gwagwarmaya.

Tsananin tsayin daka da mayakan Hizbullah da na Falasdinawa suke yi a Gaza ya sanya yahudawan sahyuniya suka firgita tare da amincewa da karfin makami mai linzami na Hizbullah da kuma rashin anfanin aikin soji akan gwagwarmayar.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta maku bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na Irna daga tashar Al-Nashrah cewa, tsohon shugaban hukumar tsaron cikin gidan yahudawan sahyoniya Geora AIland ya bayyana cewa: Yakin Gaza da Lebanon ba ya haifar da wata nasara face mutuwar wasu dayawa daga sojojin mu".

Ya kara da cewa: matsin lambar soji kadai baya kawo sakamako mai kyau Kashi 90% na sakamakon za a samu ta hanyar siyasa ne.

A sa'i daya kuma, kafofin watsa labaru na gwamnatin Sahayoniya sun yi ikrarin cewa: Kasar Lebanon ta zama filin kisa ga dakarun tawagar Golani. Abin da aka sanar a kafafen yada labarai ya yi nisa da abin da ke faruwa a zahiri.

Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun bayyana cewa: A halin yanzu kungiyar Hizbullah tana samun karin koshin lafiya, kuma har yanzu tana da tarin makamai masu linzami, wadanda galibinsu makamai masu linzami ne na gaske. Kashe sojoji 6 da aka yi jiya a kudancin kasar Lebanon ya karu akan jerin sunayen sojojin da suka mutu daga tawagar Golani, wanda ya kai 108 da suka mutu. Ana ci gaba da kashe sojoji tare da aukuwar bala'i bayan bala'i ga sjojin Yahudawa a Lebanon da Gaza.

Wadannan majiyoyin sun ce: Hizbullah tana da karfin tura miliyoyin Isra'ilawa zuwa matsuguninmafaka a kowace rana, wanda hakan zai haifar da raguwar bukatun Isra'ila a tattaunawar.

Wannan abun fa yana faruwa ne yayin da wakilin Al-Mayadeen a kudancin kasar Lebanon ya sanar da cewa, kungiyar Hizbullah ta kaddamar da sabbin hare-hare daga kasar Lebanon zuwa Mergliot a Isba al-Jalil.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, a safiyar litinin da ta gabata sojojin yahudawan sahyuniya sun kaddamar da wani gagarumin farmaki a yankuna daban daban na kudancin kasar Lebanon, wanda kuma ke ci gaba da kai hare-hare har zuwa yanzu.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ba ta yi shiru ba dangane da hare-haren da ake kai wa fararen hula a wannan kasar ba, kuma tun a farkon mintoci na farko, ta fara hare-hare da dama a kan matsugunan yahudawan sahyoniya da ke arewacin Palastinu da aka mamaye.

A cikin kwanaki da sa'o'i da suka gabata kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta yi ruwan makamai masu linzami kan wuraren da sojojin yahudawan sahyoniya suke, a sa'i daya kuma tana ci gaba da farautar sojoji da motocin sulke na maharan a yakin kasa.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a jiya Laraba cewa adadin shahidan da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa wannan kasa ya kai 3,365.

Har ila yau, a cikin wannan lokaci mutane dubu 14 da 344 ne suka jikkata sakamakon wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniya ta yi wa kasar Labanon.