Har ila yau, an jaddada batu kan batun
hakkoki, musamman hakkin 'yan gudun hijirar domin ganin dawowarsu da kuma biyansu
diyya wanda yayi daidai da dokar kasa da kasa musamman dokata 194.
A wannan qudiri bisa abunda sun jaddada amincewar tsohon taron koli da kuma bukatar fuskantar wuce gona da iri da Isra'ila ta ke yi a Gaza da Lebanon.
Saudi Arabia ta tabbatar da cewa: Manufarmu ita ce dakatar da yakin a matakin farko / domin manufofin yaƙin sun wuce tabbacin tsiran tsaron "Isra'ila".
Ministan Harkokin Waje na Saudiya ya ce: Za mu yi kokarin fahimtar da ra'ayoyin mutane zuwa ga hakkokin Falasdinawa. Mun shedi aiwatar da ta’addancin a Yammacin gabar bakin Jordan, kuma yakin yana kara fadada wanda kuma ya hada harda Lebanon.
Manufarmu ita ce dakatar da yakin a matakin farko. Don haka bai kamata mu ba da damar da al’ummar duniya zasu iya rufe idanunsa a kan ta’addancin Isra’ila ba.
Al'umman duniya suna sun yi kasa agwiwa kan hakkin da ya hau kansu ga al'amuran da suka shafi yakin a Gaza.
Zaman gaggawa na shugabannin musulinci da kasashen larabawa sun jaddada cewa muna magana a cikin murya guda game da Falasdinu da cewa: "Isra'ila ta keta doka da 'yancin ɗan adam kuma akwai hukunci da sakamako akan hakan”.
Rigingimun Falasdinawa na Isra'ila ba shi da wani mafita na soja wanda kawai mafita shi ne samar da kasashen biyu.
Yanzu akwai mafuta ta kasa da kasa ga samar da kasashen biyu. Kwamitin Tsaron kasa da kasa ya kasa shawo kai na wannan fitina. Kwamitin Tsaro sun kasa yin hulɗa tare da wannan fitina.
Manufofin yaƙin Isra’ila a Gaza ya wuce na cewa don samar da tsaro ko bawa Isra’aila tsaro ne. Muna ci gaba da matakan diflomasiyya don ganin kwanciyar hankali wanda kowa ya cancanci samun hakan. Ba a yanke qudiri kaitsaye a cikin wannan taron dangane da Gaza ba domin qungiyoyin kai da kai suke da alhakin yanayin da ake ciki yanzu.
Za mu yi ƙoƙarin tilasta Isra'ila don biyan diyyar haraji ga Kungiyoyi kai da kai, akwai kungiyoyi guda uku wadanda da yawa daga cikin kasashe suna da mamba acikinsu zamu bukaci da su yi Magana da murya daya dangane da batun Falasdinu.
Hanya mafi sauri don tallafawa Falasdinawa da kuma biyan haƙƙokinsu shine a fitar da ƙudurin tsagaita wuta na duniya. Domin Falasdinawa a Gaza da gaban kogin Joda na da bukatar goyon baya.