Tashar talabijin ta Hebrew 12 ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaro sun shawarci Benjamin Netanyahu da ya guji zama a kayyadadden wurare ko takamaiman wuraren saboda dalilai na tsaro. sun sanar da cewa bayan harin da jiragen yakin Hizbullah suka kai kan gidan Netanyahu da ke birnin Qaisaria, jami'an tsaro sun shawarci Netanyahu da kada ya zauna a wurin.
Kafafen yada labaran yahudawan sahyuniya sun bayar da rahoton cewa, wani jirgin saman yaki mara matuki na kungiyar Hizbullah ya kai hari a gidan Netanyahu inda suka ce an girke motocin daukar marasa lafiya da na 'yan sanda da dama a kusa da gidan Firayim Minista.
A halin da ake ciki kuma tashar 11 ta gwamnatin Sahayoniyya ta sanar da cewa, kai tsaye wannan jirgin mara matuki ya nufi gidan Netanyahu daga bangaren Lebanon bayan ya yi tafiyar kilomita 70, kuma ana iya ganin hayakin fashewar sa daga nesa.
Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniyya, ta nakalto wata majiya mai tushe a ofishin firaministan kasar ta wannan gwamnati, ta sanar da cewa, a lokacin da jirgin ya kai harin, Netanyahu da matarsa ba sa nan a gidansu da ke Qaisaria.
Kwana daya gabanin gudanar da wannan aiki, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, dakin gudanar da ayyukan gwagwarmayar musulunci bisa ka'idojin jagorancin gwagwarmayar, zai ba da sanarwar sauyin wani sabon mataki da ci gaba da arangama da makiya Isra'ila, wanda zata nuna kanta a cikin kwanaki masu zuwa.
Kwanaki kadan bayan harin da jiragen yakin Hizbullah na kasar Labanon suka kai a gidan firaministan gwamnatin sahyoniyawan, kafafen yada labaran wannan gwamnati sun amince da cewa wannan jirgi mara matuki ya isa dakin kwanan Netanyahu.
Bayan wannan harin ne sashen tsaro na ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gabatar da wasikar gaggawa a ranar 7 ga watan Nuwamba inda ta bukaci karin kudade da darajarsu ta kai shekel miliyan 2 (kimanin dalar Amurka 528,000) don karfafa matakan tsaro a gidan Netanyahu da ke birnin Qaisaria dake cikin Qudus da aka mamaye.