Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta bias nakaltowa daga Kamfanin dillancin labarai na kasar Labanon ya ruwaito cewa:, an kashe mutane 6 tare da raunata wasu mutane 38 a harin wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawa a birnin Taya na kasar Lebanon. Wannan kididdigar dai har yanzu ta farko ce kuma ana ci gaba da aikin kawar da tarkace na ceto rayukan wadanda wadannan hare-haren suka rutsa da su.


