Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: Majiyar Labanon Hezbollah ta yi amfani da makamai masu linzami a wannan harin. Inda ta harba makamai masu linzami 10 kuma wani makami mai linzami daga cikin wanda aka harbor ya fadi kusa da filin jirgin sama na Ben Gurion
An harba wadannan makamai masu linzami guda 10 ne a tsakiyar Falasdinu da ta mamaye a ranar da Sayyid Hasan Nasrallah ya cika kwana Arbaeen da yin shahada. Wannan harin ya sanya Sahayoniyawan miliyan daya sun gudu zuwa mafaka.
Sannan a wannan harin makamin da aka kai ya samu wata mota a Ra'ana da ke arewacin Tel Aviv.
Inda shima birnin Maalut Tarshiha da kewayensa a yammacin Galili a ya samu ruwan rokokin Hizbullah.
Bayan faruwar wannan harin kafofin yada labaran Isra'ila sun ce An dakatar da filin jirgin sama na Ben Gurion na Tel Aviv bayan harin makami mai linzami na Hezbollah.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun kara da cewa: Jirgin Boeing 777 ya lalace sakamakon tsatsauran tarwatsewa a filin jirgin sama na Ben Gurion. Sun kara da cewa Fiye da mazauna miliyan 1 sun gudu zuwa mafakarsu.