6 Nuwamba 2024 - 07:55
Kisan Gillar Da Sojojin Yahudawan Sahyoniya Suka Yi Wa Iyalan Falasdinu

Ta hanyar kai hari gidan iyalan Al-Barawi da ke Beit Lahia a arewacin Zirin Gaza, gwamnatin Sahayoniyya ta yi sanadiyyar shahadar dukkan 'yan dangin wannan gida.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: Sojojin yahudawan sahyoniya a kokarinsu na kisan kare dangi sun yi ruwan bama-bamai a gidan iyalan Al-Barawi da ke Beit Lahia da ke arewacin zirin Gaza. Wanda hakan yayi sanadiyyar shahadar Dukkan mambobi na wanna dangi.