Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: An harba tauraron dan adam na Kausar da Hudhuda na Iran zuwa sararin samaniya tare da anfani da na'urar harbawa Soyuz na kasar Rasha.
Wannan harba na’urar tauraron dan Adam shi ne yunkurin farko na kai da kai na kasar ta hanyar kerawa da harba tauraron dan adam zuwa sararin samaniya, wanda ake kallon abun wani muhimmin mataki a masana'antar sararin samaniyar Iran.
Kausar tauraron dan adam ne na'urar ganowa da sa ido ne mai daukar hoto mai inganci wanda aka kera shi don aikace-aikace daban-daban da suka hada da noma, albarkatun kasa, muhalli da magance tabarbarewar yanayi.
Hudhuda tauraron dan adam ne amma karamin tauraron dan adam ne mai dauke da aikace-aikacen sadarwa, wanda aka yi shi don ƙirƙirar hanyoyin sadarwar tauraron dan adam da Intanet da sauran abubuwa.
Wannan tauraron dan adam na iya ba da sabis na sadarwa a wurare masu nisa da wuyar isa a inda aka iyakance damar shiga hanyoyin sadarwar duniya.
