19 Oktoba 2024 - 06:48
Bidiyon Yadda Jiragen Hizbollah Marasa Matuki Suka Kai Hari Gidan Netanyahu

Majiyar Ibraniyawa ta rawaito cewa jirgin mara matuki ya afkawa yankin Qaisaria da ke yankunan da aka mamaye. Jami'an tsaro da agaji na gwamnatin Sahayoniyya sun yi gaggawar zuwa wajhen da abun ya faru, gidan Netanyahu, bayan harin da jirgin saman Hezbollah ta kai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Sharq na kasar Saudiyya ya nakalto majiyar ta cewa: Wani bama-bamai da aka yi amfani da su wajen kai hari gidan firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da ke Caesarea.

Kamfanin dillancin labaran Al-Sharq ta kasar labarawa kuma kara da cewa an aike da wannan jirgi mara matuki mai fashewa daga kasar Lebanon ne.

Dangane da wannan wakia, jaridar Yediot Aharnot ta ruwaito cewa ofishin Netanyahu ya ki bayyana inda yake a lokacin fashewar jirgi mara matuki Qaisariyya.

Tashar yada labaran sahyoniya ta Vala ta kuma ruwaito cewa, 'yan sanda da dama na kan hanyar zuwa wurin da jirgin mara matuki ya fadi.