11 Oktoba 2024 - 13:22
Bayan Ta Fitar Da Sanarwa Kungiyar Gwagwarmayar Islama Ta Iraki Ta Tabbatar Da Kai Hari A Yankin Golan Da Aka Mamaye

A daren jiya (Alhamis 10 ga watan Oktoba) kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta tabbatar da harin da jiragen yaki mara matuki suka kai a wasu yankunan Golan da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya kawo maku rahoto cewa, a daren jiya (Alhamis 10 ga watan Oktoba 2024) kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta fitar da wata sanarwa da ta tabbatar da harin da jiragen yaki mara matuki suka kai a wasu yankunan Golan da aka mamaye.

Fassarar nassin bayanin shine kamar haka:

بسم الله الرحمن الرحیم

أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُمۡ ظُلِمُواْۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصرِهِمۡ لَقَدِيرٌ

Da sunan Allah, Mai rahamam Mai jinkai.

An yi izini ga wadanda ake yaka da cewa an zalunce su, kuma lalle Allah Mai iko akan taimakon su.

A ci gaba da tinkarar mamaya da goyon bayan al'ummar Palastinu da Lebanon da kuma mayar da martani kan laifukan da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ta yi kan fararen hular Palastinu da suka hada da kananan yara da mata da tsoffi, Mujahidan gwagwarmayar Musulunci ta Iraki a yammacin yau Alhamis 10-10-2024, an cimma nufaci wata muhimmiyar kafa a Golan da aka mamaye inda aka kai hari da jirage marasa matuka. gwagwarmayar Musulunci ta Iraki tasha alwashi ci gaba da kai hare-hare kan wuraren makiya har sai an daina kai hare-haren keta iyaka nay an mamaya.

 

Kuma Tabbas ga Allah ne kawai nasara ta ke, Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.

وَمَا النَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِندِ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيم

Gwagwarmayar Musulunci a Iraki

 

Alhamis 6 Rabiu al-Thani 1446