4 Oktoba 2024 - 19:55
Duk Da Goyon Bayan Wanda Aka Zalunta Da Yazo A Tarihin Imam Ali As, Me Ya Sa Mutane Ba Su Mara Masa Baya?

Dole ne a yarda da cewa Ali (a.s.) ba wai kawai yana da kima da farin jini a tsakaninmu musulmi ba, sai dai kamarsa da ba kasafai ake samunsa ba wanda mutum ne na musamman ya cancanci yabo da girmamawa ga dukkan bil'adama.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) - ABNA- ya kawo maku cewa: Imam Ali (AS) ya kasance mutum ne mai gaskiya da adalci kuma yana son aiwatar da adalci a cikin al'umma da kwato hakkoki daga azzalumai.

A cikin wata wasika zuwa ga Malik Ashtar Nakhai, shugaban kasar Masar, Imam (a.s) ya tunatar da shi kan wannan lamari, ya kuma umurce shi da cewa: Ka ba da wani lokaci ga mabukata, da masu rauni, da talakawa, ka bar kofofin fadar mulki "Daralamareh" a bude. ta yadda mutane za su zo gare ka cikin walwala ba tare da cikas ba, su fada maka matsalolinsu, ta yadda kai da kanka ka zaka kula da matsalolinsu; Domin naji sau da yawa daga Manzon Allah (SAW) yana cewa:

Al'ummar da ba ta karbar hakkin masu rauni a fili ba tare da tsoro ba, ba za ta taba yin tsarki ba kuma ba za ta taba ganin fuskar farin ciki ba (1).

Imam Ali (A.S.) Yana Kan Kololuwar Mataki Wajen Inganta Adalci Da Kare na kasa da shi wanda kuma ba tare da kawaici da kyaliya ba, shi ma yana lissafta ayyukansa da ya aikata, ya kuma ladabtar da azzalumai, ya mayarwa musu da hakki garesu, ya kuma yi babbar murya da azama yana mai cewa: A wurina, mai rauni wanda aka zalunta ya zama abin soyuwa ya karbi hakkinsa, kuma mai karfi azzalumi kaskance ne mai rauni a idona wajen in karbi hakkin wasu daga gare shi. Mun gamsu da umarnin Allah kuma mun mika wuya ga umurninsa (2).

Bayan da Imam (a.s) ya karbi matsayin halifanci ya yi kokarin kawar da azzaluman shugabanni daga cikin al'amuran musulmi, kuma ya kasance mai tsayin daka da azama a kan wannan hukunci.

Don haka dangane da Ibn Abbas, wanda yake adawa da sauke Mu’awiyah daga mulki, ya kuma shawarci Imam da ya yi sulhu, inda ya ce: “Bai dace a cire Mu’awiyah a halin yanzu ba, sai Imam ya amsa musa da cewa:

“Ko da rana daya ba zan iya ganin masu mulki lalatattun mutane masu rashin cancanta suna shugabantar al’ummar Musulmi ba (3).

A lokacin halifancinsa Ali (a.s) ya so ya dakatar da kwadayin taska da dukiyar al’umma da tsarin zalunci da aka samar da shi wajen rabon baitulmali da mayar da al’ummar musulmi zuwa ga daidaito da tsarin zamanin Manzon Allah (s.a.w).

Wannan wani abu ne da manyan kuraishawa da mawadata na Hijaz da masu dukiya ba su taba yarda da shi ba. Domin sun san cewa Imam (a.s.) yana kallon kowa daidai ne wajen rabon baitulmali.

Imam (a.s) ya tsaya a gaban dukkan wani makirci da suke kuma bai wuce tafarki madaidaici ba ya amsa musu da hankali da tunani.

A wani lokaci sayyidina Ali (A.S) ya kasance yana raba haraji da ma’auni a tsakanin musulmi. Wani shahararren mutum ya fito daga Ansar sai Imam (a.s.) ya ba shi dinari uku, bayansa kuma sai wani bakar fata. Imam (a.s) shima kuma ya ba shi dinari uku.

Sai mutumin Ansari ya ce yana adawa da hakan yana cewa: Ya Amirul Muminin! Wannan bawana ne da na 'yanta jiya, ka mai da shi daidai da ni?!

Dangane da wannan mutumin Ansari Imam (a.s) ya ce: Na duba littafin Allah, ban ga wani fifiko ga ‘ya’yan Isma’il a kan ‘ya’yan Is’haka ba.

Hakika kamar yadda dukan mutane ba’a haifesu bayi da baiwa daga Adam dukkansu ’yantattau ne.

Sai dai kuma abin bakin cikin shi ne, irin wannan mu’alama ta Imam (AS) ba ta yiwa mutanen da suka saba da tsarin nuna wariya na tsawon 1%4 dadi ba, don haka suka rika adawa da shi, har suka kai ga a karshe sun yake shi.

A cikin Bihar, Allamah Majlisi ya kawo daga littafin “Da’awat Rawandi” inda ya nakalto daga “Ali bin Ja’ad” yana cewa: Babban abin da ya sa Larabawa suka daina ba wa Amirul Muminin Ali (AS) goyon baya shi ne harkokin kudi ne. Domin kuwa bai taba fifita mai daraja a kan mara daraja da Balarabe a kan wand aba balarabe ba.

Kuma bai kebance kaso na musamman ga shuwagabanni da kwamandojin qabilu ba – kamar yadda sarakunan gabaninsa suka yi – kuma bai jawo wa kansa kowa ba ta hanyar kudi, alhali kuwa Mu’awiya ya aikata gaba dayan hakan ma;ana sabanin abun Imam Ali As yayi.

________________________________________________

 

Madogara:

1- Nahjul-Balaghah, Subhi Salih, wasika ta 53.

2- Nahjul-Balagha, Huduba ta 37.

3- Littafin:  Wanene Ali?, shafi na 212.

4- Al-Kafi, juzu’i na 8, shafi na 69, h 26.

5-Bihar al-Anwar, juzu'i na 41, shafi na 133.