8 Yuli 2025 - 01:21
Source: ABNA24
Hamas: Ta Aiwatar Da Munana Hare-Hare Kan Sojojin Isra'ila / Sojoji 5 Sun Mutu Sama Da 20 Sun Jikkata An Yi Garkuwa Da 3

Kafofin yada labaran Isra'ila sun tabbatar da aukuwar mummunan tarko ga sojojinsi inda kisan biyar suka mutu 20 da yan kai suka jikkata. Daya daga cikin wadanda suka jikkata a lamarinwani babban jami'in hafsan Isra'ila ne.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baity (As) -Abna- ya bayar da rahoton cewa: Sojojin Isra'ila sun faɗa tarkon bama-bamai hudu a jere a arewacin Gaza

Kafofin yada labaran Isra'ila sun kaso cewa da farko an jefa wani bam kan tankar sojoji, sannan bam na biyu aka jefa shi kan jami'an ceto da suka zo domin ceto mutanen da ke cikin tankar, daga karshe kuma bam na uku ya auka wa wasu karin jami'an ceto da aka aike domin taimakawa.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ba da rahoton cewa, bayan da bama-bamai uku suka tashi a arewacin Gaza, bam na hudu ya tashi, kana anji ruwan kananan bindigogi suka nufi dukkan wadanda suka samu raunuka na farko a harin.

Abin lura shi ne cewa an gudanar da wannan aiki ne a arewacin Gaza, inda yahudawan sahyoniya suka ce an kawar da su gaba daya!

Karar fashewar kwanton bauna na mayakan Hamas na da matukar ban tsoro da karfi har aka ji har zuwa birnin Ashkelon

Hamas ta iya kama wani sojojin yahudawa a wannan tarkon. Kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun rawaito cewa wansu sojojin wannan gwamnatin sun bata bayan wannsn mummunan harin kwantan bauna da kungiyar Hamas ta kai.

Sannan Majiyoyi na yaren yahudanci sun sanar da faruwar lamarin tsaro a arewa maso gabashin Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza cewa an kai hari da wata mota kirar jeep ta soji, g wata mota kirar buldoza D9 da wata tankar Merkava tare da cinna mara wuta. A cewar wadannan majiyoyin, lamarin ya yi yawa fiye da yadda ake tsammani kuma sojojin na ci gaba da neman sojojin uku da suka bata.

Wasu majiyoyi sun jaddada cewa alkaluman baya-bayan nan sun nuna cewa sama da sojojin Isra'ila 20 ne aka kashe tare da jikkata a wannan samame.

An kai farmakin ne kan dakarun Nahal Brigade, wadanda aka baiwa alhakin kula da yankin arewacin zirin Gaza kwanakin baya.

A cikin wani karin rahoto kan mummunan lamarin da aka samu kan sojojinta, kafar yada labaran yahudawan sahyoniya ta sanar da cewa:

Kokarin kubutar da sojojin uku da suka bata ya fuskanci hare-haren Qassam. Arewacin Gaza yana ganin zoben wuta da hargitsi na gaske.

Rikicin ya ci gaba da tsananta inda sojoji uku suka bace tare da kona motocinsu.

Sojojin da aka kaiwa hari sun fito ne daga wata runduna ta musamman ta "Nahal" wacce ta shiga arewacin Gaza kwanaki kadan da suka gabata

Anji cewa Netanyahu ya bar ganawar da suke yi da Witkaf ya katse biyo bayan lamarin tsaro a arewacin Gaza

Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayyana cewa, bayan samun rahotannin gaggawa game da lamarin a arewacin zirin Gaza, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya katse ganawarsa da wakilin shugaban Amurka Witkaf, domin samun cikakken bayani kan lamarin.

Zuwa yanzu Jiragen yakin Isra'ila na kai hare-hare da yawa a Gaza

Al-Qassam kuma sun ce zasu saki Bidiyon harin kwanton bauna da aka kai daren yau a Beit Hanoun nan ba da jimawa ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha