4 Oktoba 2024 - 10:58
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Kada Ku Yanke Tsammani Kada Ku Shiga Firgici, Kada Ku Yi Shakka A Kan Tafarkin Gwagwarmaya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Gwagwarmaya da ake yi a zirin Gaza ya sanyawa janyo idanun duniya sosai tare da baiwa Musulunci girma.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti - Abna: Haka nan kuma yayin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ke ishara da muhimmin sakon Sayyid Hasan Nasrallah ga al'ummar kasar Labanon a yayin da aka rasa wasu fitattun masu gwagwarmaya ya cewa: kada ku yanke tsammani da shiga firgici, kada ku yi shakka a kan tafarkin gwagwarmaya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci a yayin da yake yin huduba da larabci a sallar Juma'a a Tehran ya ce:

Mafi Mahimmancin sakonsa na bayanansa da aikinsa a rayuwarsa ta duniya gare ku ya ku al'ummar kasar Labanon, kada ku yanke fata da shiga damuwa sakamakon rasa manyan mutane irin su Imam Musa Sadr da Sayyid Abbas Musawi da sauransu; Kada ku yi shakka a tafarkin gwagwarmaya; Ku Ƙara iyawarku da ƙarfin ku ninka hadin kan ku; Ku fuskanci maƙiya masu zalunci wajen gwagwarmaya ta hanyar ƙarfafa bangaskiya da tawakkali.

Masoyana! Al'ummar Lebanon masu aminci! Matasa masu kishin Hizbullah da Amal! 'Ya'yana! A yau abin da shahidinmu Sayyid ya ke so kenan daga al’ummarsa, da bangaren gwagwarmaya, da sauran al’ummar musulmi baki daya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Duk wani hari da aka yi wa gwamnatin Sahayoniya hidima ce ga dukkan bil'adama.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Gwagwarmaya da ake yi a zirin Gaza ya sanyawa janyo idanun duniya sosai tare da baiwa Musulunci girma.