21 Oktoba 2026 - 20:52
Source: ABNA24
Ayatullah Ramezani: Gwagwarmaya Ainihin Rahama Ce

An gudanar da taron kimiyya na farko na babban taron ƙasa da ƙasa "Allama Shahidi Sayyid Hassan Nasrallah" wanda ya mai da hankali kan sake bitar rawar da wannan shahidi maɗaukaki ya taka a fagen ƙasa da ƙasa da duniyar Musulunci, tare da halartar gungun manyan mutane na hauza da jami'a a Qom. Masu jawabi a wannan taron, sun nazarci sassan halin rayuwar shahidi Nasrallah da ba a san su sosai ba tun daga fannin fikihun gwagwarmaya, falsafa, gudanarwa na dabarun da bin jagorancin faqihi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ayatullah Ramezani a cikin wannan taron farko tare da yin nuni ga kalaman Jagora Mai Girma na juyin juya hali kan manyan mutane ya bayyana: Imam Shahidi ya yi amfani da kalmar "makaranta" kan mutane biyu kuma kalmar "Alama" kan mutane biyu; shahidi Haji Qassem Soleimani da shahidi Sayyid Hassan Nasrallah.

Babban sakataren Majalissar Ahlul-Bayt (AS) ta Duniya tare da nanata cewa shahidi Nasrallah ya kafa wani yunkuri na wayewa ya ƙara da cewa: fikihun gwagwarmaya a cikin gogewar shahidi Nasrallah, wata fasaha ce ta iko wadda take da matakai na fikihu, ɗabi'a, dabaru da tsari.

Ya ƙara da cewa: Gwagwarmaya a cikin tunaninsa ba wai ta kasance wani ra'ayi ne na soji kawai ba, a'a sai dai tana samun ma'ana a rayuwar jama'a cikin adalci da samar da amincewa.

…………….

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha