A cikin kwanaki 10 na baya-bayan nan, kimanin 'yan gudun hijira dubu biyar daga yakin Lebanon sun shiga Iraki daga tashar jiragen sama na Bagadaza da Najaf Ashraf da ma kan iyakar Al-Qaim.
A baya dai gwamnatin kasar Iraki ta sanar da samar da kayayyakin da ake bukata ga 'yan gudun hijirar Lebanon da za su yo tafiya zuwa Iraki da kuma zama a wannan kasa har zuwa karshen yakin da ake yi a kasar Labanon. Harami mai tsarki na Imam Husaini As ya kuma sanar da cewa yana karbar 'yan gudun hijirar Lebanon a biranen da ake kai ziyara da sauran wuraren kwana na wannan Haramin.