2 Oktoba 2024 - 11:23
An Harba Makaman Roka 100 Cikin Sa'o'i Kadan / Sojojin Yahudawan Sahyoniya Sun Ja Da Baya Karkashin Hare-Haren Hizbullah.

Tashar talabijin ta 13 ta gwamnatin Sahayoniyya ta bayar da rahoton cewa, a cikin 'yan sa'o'i da suka gabata an harba makaman roka 100 daga kasar Labanon zuwa arewacin Palastinu da aka mamaye.

Tashar talabijin ta 13 ta gwamnatin Sahayoniyya ta bayar da rahoton cewa, a cikin 'yan sa'o'i da suka gabata an harba makaman roka 100 daga kasar Labanon zuwa arewacin Palastinu da aka mamaye.   

A lokaci guda kuma rundunar sojojin kasar Labanon ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin sahyoniyawan sun karya layukan da ake kira blue line (tsarin layin majalisar dinkin duniya tsakanin Palastinu da arewacin kasar aka mamaye da kuma kudancin kasar Lebanon) inda suka kutsa cikin kasarmu a yankunan Yaron da Bawaba da -Adisa, amma sun koma tare da ja da baya.

A baya dai kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da kai harin kwanton bauna kan hanyar dakarun yahudawan sahyoniya a yankin Al-Adisa.

Majiyoyin labarai na gwamnatin sahyoniyawan sun tabbatar da cewa a wannan harin kwantan bauna an kashe sojojin yahudawan sahyoniya akalla 4 tare da jikkata wasu 20 na daban.

Shugaban sashen yada labarai na kungiyar Hizbullah Muhammad Afif ya bayyana cewa: A yakin na yau an kashe sojojin yahudawan sahyoniya da dama, kuma gwamnatin yahudawan sahyoniya ta shiga tsaka mai wuya dangane da hakan.

Yace: "Abubuwan da suka faru a Mosghaf Aam da Marun al-Ras da Al-Adisa somin tabi ne".