2 Oktoba 2024 - 05:22
Sojojin Yahudawan Sahyoniya Sun Fada Tarkon Mayakan Hizbullah

Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan a safiyar yau Laraba sun bayar da rahoton harin kwantan bauna da mayakan Hizbullah suka yi ga sojojinsu a yankin kan iyaka na kudancin Labanon da kuma arewacin Palastinu da aka mamaye.

A cewar wadannan kafafen yada labarai, an jikkata wani adadi mai yawa na sojojin yahudawan sahyoniya a wannan harin kwantan bauna.

Sannan Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin sahyoniya ta sanar da cewa, an harba rokoki akalla 30 daga kudancin kasar Labanon zuwa matsugunan yahudawan sahyuniya a yankin Al-Jalil da ke arewacin Palastinu da ta mamaye.

Sannan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar bayani dangane da harba makaman roka na Barkan zuwa matsugunan yahudawan sahyoniya na "Shtola"

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba cewa: Mayakan mu sun kai hari kan matsugunan sahyoniyawan "Shatola" da makamai masu linzami na Barkan tare da yin barna ga 'yan mamaya.