Sojojin gwamnatin Qudus da ke mamaya sun fara kai hare-haren wuce
gona da iri kan yankunan Al-Wazani da Dasht Khayyam sa'o'i biyu da suka gabata,
wanda har yanzu ake ci gaba da kai hare-hare.
A halin da ake ciki kuma, sojojin kasar Labanon na kwashe kayayyakin sa ido a kan iyakar kasar da Falasdinu da aka mamaye domin shiga wasu yankuna masu nisa a garuruwan kan iyaka.
NBC News ta ruwaito daga wani jami'in Amurka cewa, Isra'ila ta aike da birged biyar zuwa kan iyaka, ko da yake ba duka ake sa ran za su motsa ba, kamar yadda NBC ta ruwaito,.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya sanar da cewa: Sojojin kasar Lebanon sun ja da baya a nisan kilomita 5 daga kan iyaka.
Duk da wata majiyar soji ta shaidawa kafar yada labaran kasar Lebanon ta LBCI cewa: Bayanin janye sojojin da aka yi har zuwa nisan kilomita 5 ba gaskiya ba ne, sai dai sun canja kayayykin aikin da aka jibge a kan iyaka zuwa manyan cibiyoyi.
Gwamnatin yahudawan sahyoniya na amfani da bindigogin igwa, phosphorus da tankokin yaki wajen kai hare-hare
Da alamu yaki karo na uku ya fara a hukumance tsakanin kasar Labanon da gwamnatin sahyoniyawa.
Tankokin gwamnatin sahyoniyawan sun shiga kasar Lebanon ne ta mashigar Metula.
Mahmoud Qomati, memba a majalisar siyasa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon: Idan wannan yaki ya yadu to kawayenmu ma za su dauki mataki.
Yediot Aharonot ya nakalto wani babban jami'in yahudawan sahyoniya ya ce: Babu yadda za a yi mazauna arewa su koma sai ta hanyar kawar da kungiyar Hizbullah, kuma ba za a iya cimma hakan ba sai ta hanyar ayyukan yakin kasa.
Sannan kungiyoyin gwagwarmayar Iraki sun sanarda shirinsu fadin kasar.