Rahoton da kafar yada labarai ta
Al-Arabiya ta fitar kan cikakken bayanin kisan Sayyid Hassan Nasrallah.
A yammacin Juma’a Dahiyat dake kudancin Labnon ya kasance wakwai taron sirri na jagororin Hizbullah a cibiyarsu dake da kariya a karkashin kasa’ wanda ya zamo yan liken Isra’ila suna sama suna kallon wajen sun dakon wajen da lokacin wanda ya zamo TelAviv ta qudiri aniyar yin kisan ne tun ranar Litinin da ta gabata.
A yau kuma juma’a itace ranar zartarwar dukkan masaniyar da take kaiwa zuwa Isra’ila sun tabbatar da cewa daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Sayyid Hasan Nasrullah kuma tabbas Sayyid din ya halarci wajen bayan shigarsu wajen gine-ginen ga sunan guda shida amma Isra’la bata san a ina za’a gabatar da taron ba shi yasa tayi ta luguden bama-bamai akan gine-ginen har sai da ta tabbatar da wani mai rai a yankin wajen wanda sun tabbatar da yana wajen tare da sauran jagororin Hizbullah. Karfe shida na aymma agogon Berut sai kawai ruwan bama-bamai da ya girgiza yanking aba daya wanda Isra’ila ta jefa bom guda 84 nau’in Mk daga saman jiragen yaki nau’I F-15I hakan ya sanya gine-ginen suka koma kamar babu su sun baje su da kasa bata bai koda alamu na wani rai da ke cikin ta ba.
Amma su da suka zartar da harin nan take bayan aiwatar da shi suka sanar da cewa babu damar rayuwa ga wadanda suke cikin wadannan gine-ginen.
