Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya habarta cewa: Jiragen yakin gwamnatin
sahyoniyawan sun yi ruwan bama-bamai a yankin da ke kusa da filin jirgin sama
na Beirut a karo na biyu cikin sa'o'i da suka gabata.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na nuni da cewa mayakan na Isra'ila sun kai hari a yankunan kudancin birnin Beirut fiye da sau 30.
Wakilin Al-Mayadeen ya jaddada cewa, a cikin sa'o'i kadan da suka gabata an kai hare-hare da dama daga bangaren 'yan mamaya na yahudawan sahyoniya kan wasu gine-ginen da ke yankunan kudancin birnin Beirut.