Ba gaskiya ba ne labarin shahadar
Hujjatul-Islam Wal Muslimin, Sayyid Hasan Nasrallah, babban sakataren kungiyar
Hizbullah ta kasar Labanon, a harin bam da aka kai a Dahiyat birnin Beirut.
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya habarta cewa: Majiyoyin da ba na hukuma ba daga kasar Lebanon sun ruwaito tabbacin lafiyar Sayyid Hasan Nasrallah a wata hira ta musamman da ta yi da kamfanin dillancin labarai na ABNA.
A daren jiya ne dai bayan harin bam a unguwar Hareh Harik da ke gundumar Dahiya a birnin Beirut da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka yi ta yada jita-jita game da shahadar babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.