Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) -
ABNA- ya habarto maku cewa: a cikin 'yan sa'o'in da suka gabata, bayan munanan
hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a birnin Beirut, jiragen yakin
yahudawan sahyoniya sun kai hari a wasu wurare a yankunan kudancin birnin
Beirut, inda suka lalata gine-gine 4 sun lalace da ruhujewa gaba daya. Tun da
sanyin safiya ake ta samun rahotannin harin da aka kai kan babban sakataren
kungiyar Hizbullah a kasar Labanon da kuma wasu manyan jagororin kungiyar
Hizbullah.
Hukumar Gidan Rediyo da Talabijin ta Isra'ila ta sanar da cewa, inda ta nakalto daga majiyar soji; Kawo yanzu dai ba a iya tabbatar da kasancewar (Sayyid Hasan) Nasrallah a hedikwatar Hizbullah a lokacin harin ba. Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya ambato wani jami'in soji yana cewa; Ƙididdiga na farko ba su isa tabbatarwa ko musanta nasarar harin da aka nufi kashe Nasrallah ba. Tashar Isra'ila ta 12: Sojojin Isra'ila za su binciki yiwuwar kasancewar Nasrallah a yankin da aka kai harin.
Buga labarin harin da wasu kafafen yada labaran Isra'ila suka kai kan babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon na nuni da wata makarkashiyar da jami'an leken asiri suka yi na gano babban wuri da majiyoyi na kusa da jagoran gwagwarmayar.
Bisa la'akari da maganganun da masu fafutukar yada labaran da suke goyon bayan Hizbullah a sararin samaniya kafofin sada zumunta, wadanda suka shafe shekaru suna gwagwarmaya da dukkanin makirce-makircen gwamnatin sahyoniyawan; Yada jita-jita na kisan Sayyid Hasan Nasrallah (Hp) a harin da aka kai a birnin Beirut na daga cikin wani shiri na "kokarin" leken asiri ta hanyar samar da manyan hanyoyin sadarwa daga majiyoyin sirri da na jama'a daban-daban da ake aiwatarwa a yankin, domin kowa yana neman bayanai daga lafiyar Sayyid Hasan Nasrallah "ta hanyar majiyoyi na kusa da Sayyid shugaban gwagwarmayar Hizbullah ne."
Wadannan majiyoyin sun jaddada; Wannan shi ne abin da makiya Isra'ila da Amurka suke sanyawa kai tsaye domin shiryawa wani yunkuri na kisa na hakika a lokacin yakin da ake yi a halin yanzu, don haka a irin wannan yanayi kowa ya jira bayanin karshe na Hizbullah.