27 Satumba 2024 - 20:06
An Musanta Labarin Shahadar Shugaban Majalisar Zartarwa Ta Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Labanon

An karyata shahadar Hujjatul Islam Wal Muslimin Sayyid Hashim Safiyuddin.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) - ABNA- ya habarto maku cewa: majiyoyin yada labaran yahudawa sun tabbatar da mutuwar Hujjatul-Islam Wal musulimin Sayyid Hashim Safiyuddin shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon bayan harin bam yankunan kudancin birnin Beirut.

Sai dai kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon cewa ta yi watsi da shahadar Hujjatul-Islam Wal Muslimeen Safiyuddin shugaban majalisar zartarwar kungiyar ta Hizbullah.

Sa'a guda da ta gabata ne sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka yi ruwan bama-bamai a unguwar Harare Harik da ke kudancin birnin Beirut da nufin kai hari kan hedkwatar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da ke karkashin kasa bisa kididdigar farko da aka yi, mutane 2 ne suka yi shahada tare da jikkata wasu 76 a cikin wannan harin ta sama.

Kafofin yada labaran yahudawan sun bayyana cewa manufar sojojin gwamnatin sahyoniyawan na kai hari a kudancin kasar Lebanon shi ne samar da wani yanki mai kariya da katangar ganuwa da suke ake da iko da ita kai tsaye.