Sakamakon harin da ba a taba ganin irinsa ba da kuma gagarumin harin da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a yankunan da ke Dahiyatu a birnin Beirut, an samu barna mai yawa a yankin.
Kafafen yada labarai sun bayyana wannan harin a matsayin wani babban kisan kiyashi mai karfin barna sosai.
Majiyoyin yahudawa sun bayyana cewa, wanda aka kaiwa harin shi ne Sayyid Hasan Nasrallah da manyan kwamandojin Hizbullah ta kasar Labanon.
