27 Satumba 2024 - 17:15
Da Dumi Dumi: Sayyid Hasan Nasrullah Yana Na A Raye Cikin Koshin Lafiya

Wannan rahoton yana dauke da biidiyon irin Barna mai yawan gaske na harin Isra'ila a Dahiyat birnin Beirut

Majiyoyin Labarai sun tabbatar da cikakkiyar lafiyar Sayyid Hasan Nasrallah

Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto cewa majiyar kungiyar Hizbullah ta kuma rubuta cewa: Sayyid Hasan Nasrallah yana cikin koshin lafiya kuma yana a waje mai aminci.

Wakilin Watsa labarai na Iran ya bayar da rahoton cewa, wasu majiyoyin Lebanon sun sanar da cewa, Sayyid Hasan Nasrallah ba ya cikin gine-ginen da aka kai harin.

Wasu majiyoyi na kusa da kungiyar Hizbullah sun kuma bayyana a cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Sayyid Hasan Nasrallah yana nan da ransa kuma yana cikin koshin lafiya.