25 Satumba 2024 - 19:59
Bidiyon Nasarar Harin Da Dakarun Islama Na Kasar Iraki Suka Kai Tashar Jiragen Ruwa Ta Eilat A Kasar Isra'ila/ 2 Sahayoniyawa Sun Samu Raunuka Sakamakon Harin Da Jiragen Yakin Suka Kai

Tashar jiragen ruwa ta Eilat ta kasance hadafin babban hari da jiragen yaki mara matuki na kasar Iraki suka kai.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) - ABNA- ya habarto maku cewa, majiyoyin yada labarai sun sanar da nasarar kai hari da jiragen yaki marasa matuki na mayakan Islama na Iraki a tashar jiragen ruwa na Eilat da ke kudancin yankunan da aka mamaye.

A cewar wannan rahoto, daya daga cikin jiragen da aka harba zuwa tashar jiragen ruwa na Eilat ya afkawa tashar, inda ya jikkata wasu sahyoniyawan biyu.

Tsarin kariya na gwamnatin sahyoniyawan ya gaza wajen katse jirgin maras matuki da gwagwarmayar Musulunci ta Iraki ta harba.

Ta hanyar buga wata sanarwa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta dauki alhakin harin da jiragen yakin kasar Iraki suka kai kan birnin Eilat da ke cikin kasar Palastinu da aka mamaye tare da jaddada ci gaba da gudanar da ayyukanta na nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da Lebanon kan gwamnatin sahyoniyawa.

Kafofin yada labaran yahudawan sun kuma bayar da rahoton cewa, harin da aka kai a tashar jiragen ruwa na Eilat ya shafi masana'antun potash (phosphate solution) ne kuma ya haifar da mummunar barna wanda ya hana fitar da shi daga Isra'ila.