24 Satumba 2024 - 18:25
Hizbullah Ta Fitar Da Bayani Dangane Da Shiga Wani Sabon Matakin Yaƙi Da Gwamnatin Sahyoniyawa

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta jaddada gwagwarmayarta a yau Talata wajen kare al'ummar Palastinu da ake zalunta tare da shiga wani sabon mataki na yaki da gwamnatin sahyoniyawa.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) - ABNA- Ya habarto maku bisa nakaltowa daga Kamfanin dillancin labaran Irna cewa, a cikin wannan takaitaccen bayani an jaddada kare wajibcin kare al'ummar zirin Gaza masu juriya da goyon bayan yan gwagwarmaya masu girma da daukaka tare da kare kasar Labanon da al'ummarta.

Wasu masana harkokin siyasa na ganin cewa kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon tana nufin wani sabon mataki na yaki da gwamnatin sahyoniyawan da ke kashe fararen yara da mata a cikin wannan bayani.

A farkon bayanin nata, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta yi ishara da aya ta 39 a cikin surah mai albarka ta Hajj cewa: “an izini ga wadanda ake yaƙa da cewa tabbas an zalunce su, kuma lalle Allah yana da ikon taimaka masu"

«أُذِنَ لِلَّذِینَ یُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُم ظُلِمُواْ وَ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَیٰ نَصرِهِم لَقَدِیر»

Har ila yau, a karshen wannan bayanin yazo cewa a cikin aya ta 126 a cikin suratu Ali-Imrana cewa: “Babu wata nasara face daga wurin Allah, Mabuwayi, Mai hikima”.

«وَمَا النَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِنْدِ اللَّهِ الْعَزِیزِ الْحَکِیمِ»

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon ta sanar a wani sabon kididdiga da ta yi a yammacin yau cewa, tun bayan fara kai hare-hare ta sama na gwamnatin sahyoniyawa a kasar Labanon, mutane 585 ne suka yi shahada yayin da wasu 1,835 suka jikkata, wadanda suka hada da yara 50 da mata 94.

Rahotanni daga kafafen yada labaran kasar sun ce mutane 113 ne suka yi shahada yayin da wasu fiye da 500 suka jikkata a cikin sa'o'i 24 na hare-haren da gwamnatin sahyoniya ta kai a yankin Bekaa da ke gabashin kasar Lebanon.