24 Satumba 2024 - 12:04
Kimanin Mutane 500 Ne Suka Yi Shahada, 2000 Suka Jikkata A Hare-haren Da Isra’ila Ta Kai Lebanon

Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, sakamakon harin da Isra'ila ta kai a ranar Litinin, mutane 500 ne suka yi shahada, yayin da wasu akalla 1645 suka jikkata.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) - ABNA- Ya habarto mamu cewa: Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, sakamakon harin da Isra'ila ta kai a ranar Litinin mutane 500 ne suka yi shahada, yayin da wasu akalla 1645 suka jikkata.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da samun karuwar shahidan na harin da gwamnatin sahyoniyawan ke kai wa a kudancin kasar.

Cibiyar agajin gaggawa ta ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, ci gaba da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kan garuruwa da kauyukan kudancin kasar ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 500. akwai yara da mata da masu aikin ceto cikin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata.

Ma'aikatar ta jaddada cewa mutane 1,645 ne suka jikkata a jerin hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon.

An kai hari ga garuruwa da ƙauyuka da wuraren buɗe ido a ko'ina cikin yini a gundumomin Sidon, da Marjayoun, da Nabatieh, da Bint Jbeil, da Taya, da Jezzine, da Zahrani a kudancin Lebanon, da kuma gundumomin Zahle, da Ba'albek, da Hermel a cikin yankin Bekaa Valley.