23 Satumba 2024 - 19:02
Kungiyar Hizbullah Ta Kai Wani Mummunan Hari Birnin Haifa

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai wani kazamin harin roka kan tashar jiragen ruwa na Haifa da ke arewacin yankunan da aka mamaye.

Kamfanin Dillancin Labaran Kasa Da Kasa Na Ahlul-Baiti As - ABNA Ya Habarta Cewa: mayakan Hizbullah na kasar Lebanon sun kai hari kan tashar jiragen ruwa ta birnin Haifa da ke arewacin yankunan da aka mamaye da wani makami mai linzami a karon farko tun bayan yakin shekara ta 2006.

Sakamakon harin makami mai linzami, an tilastawa 'yan sahayoniya 300,000 a Haifa tserewa zuwa matsugunan karkashin kasa.

Bayan harin makami mai linzami na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, an ji karar fashewar wasu abubuwa a yankuna daban-daban na birnin Haifa.

Babu wani rahoto da aka buga kan adadin hasarar rayuka ko asarar dukiya da aka yi na wannan katafaren harin makami mai linzami.

Birnin Haifa dai shi ne birni mafi girma a arewacin yankunan da aka mamaye, wanda ke da daya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa na gwamnatin Sahayoniya, kuma birnin Haifa na taka rawa sosai a tattalin arzikin Isra'ila.