Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya bayar da rahoton cewa:
a ranar Lahadi 22 ga watan Satumba ne dakarun gwamnatin sahyoniyawa su kai
samame ofishin gidan talabijin na "Al Jazeera" da ke birnin Ramallah
da ke yammacin gabar kogin Jordan tare da bayar da umarnin rufe ofishin wannan
kafar yada labarai ta Qatar na tsawon kwanaki 45.
