A cikin jawabin da ya gabatar a yau dangane da wani canji da aka samu a yankin da kuma kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa:
A ranar Talata ne aka samu sakonni ta kafafen yada labarai na hukuma da wanda bana hukuma ba cewa makasudin harin da Isra'ila ta kai na (ayyukan ta'addanci a Labanon) shi ne dakatar da dakarun kasar Labanon wajen taimakawa Falasɗinu amma muna jaddada cewa kungiyar ta Lebanon ba za ta dakata ba, kuma za ta ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar Palasdinawa.
Tel Aviv ta yi magana game da samar da kulli na tsaro a cikin Labanon kuma muna fatan za ta yi hakan. A gare mu, duk wani kutse cikin ƙasar Labanon zai zamo wata dama ce ta tarihi don kai hari ga abokan gaba, wanda zai yi tasiri mai yawa a fagen yaƙi. Wannan yunkuri na kwamandan yankin arewacin Sahayoniya na wauta ne.