Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya habarta cewa: kungiyar gwagwarmayar
Musulunci a kasar Lebanon ta fitar da sanarwa bayan harin ta'addancin da
yahudawan sahyoniyawan mamaya suka kai.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a cikin bayaninta ta tabbatar da cewa gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon a yau da gobe kamar sauran dukkanin kwanakin da suka gabata za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta masu albarka na tallafawa Gaza da al'ummarta da gwagwarmaya da kuma kare kasar Labanon da al'ummarta da kuma shugabancinta. "Wannan tafarki yana na ci gaba da wanzuwa, kuma ya sha bamban da sakamakon mai tsanani da yake jira makiya masu laifi sakamakon kisan gillar da suka yi a ranar Talata a kan al'ummarmu, da mutanenmu, da kuma mujahidanmu a Lebanon, wannan kuma wani hisabi ne daban da zai zo nan gaba Da yaddan Allah".
Har ila yau gwagwarmaya ta bayyana a cikin sanarwar mafi girman ta'aziyya ga iyalan shahidan masu daraja da suka rasu a jiya Talata, a dukkan bangaren kudu a Blida da Majdal Salam ko kuma shahidan da suka mutu a cikin ta’addancin wuce gona da iri ta hanyar jefa bam na hanyoyin sadarwa (pagers), muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.
gwagwarmaya ta karkare bayanin ta da cewa: "Abin da ya faru a jiya zai kara mana azama da jajircewa wajen ci gaba a kan tafarkin jihadi gwagwarmaya, kuma muna da cikakken yakinin cikar alkawarin Allah Madaukakin Sarki na nasara da ya yi wa muminai mujahidai masu hakuri, in Allah Ya yarda".