10 Mayu 2025 - 11:57
Source: ABNA24
Sojojin Pakistan Sun Kaddamar Da Farmakin Soji A Matsayin Martani Ga Harin Da Indiya Ta Kai.

Tashar talabijin ta Pakistan ta bayar da rahoton cewa, farmakin da aka yi wa lakabi da "Operation Solid Structure" ya lalata wani wurin ajiyar makamai masu linzami na BrahMos a Beas da kuma sansanin jiragen sama na Pathankot da Udhampur a Indiya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa na Ahlulbayt (As) –ABNA- ya bayar da rahoton cewa:, Pakistan ta kaddamar da farmakin soji da sanyin safiyar Asabar a matsayin martani ga harin da Indiya ta kai. Islamabad ta ce Indiya ta harba makamai masu linzami zuwa muhimman cibiyoyin soji, a dare na uku da aka yi arangama mafi girma a tsakaninsu cikin shekaru da dama da suka wuce.

Tashar talabijin ta Pakistan ta bayar da rahoton cewa, farmakin da aka yi wa lakabi da "Operation Solid Structure" ya lalata wani wurin ajiyar makamai masu linzami na BrahMos a Beas da kuma sansanin jiragen sama na Pathankot da Udhampur a Indiya.

Sabanin haka, CNN ta ruwaito wani jami'in Indiya yana cewa a halin yanzu Indiya tana mayar da martani ga hare-haren Pakistan da yanayin daya dace.

Jaridar New York Times ta kuma ruwaito jami'an sojin Indiya na cewa sojojin Pakistan sun yi yunkurin kutsa kai cikin wurare 36, inda suka yi amfani da jirage marasa matuka 300 zuwa 400 wajen gwada matakan tsaron da Indiya ke dauka.

Kafofin yada labaran Indiya sun ba da rahoton cewa wasu fashe-fashe guda shida sun afku a birnin Srinagar da ke yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya kuma bayyana cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa a garuruwan Amritsar da Jammu.

A cewar hukumar, jami'an tsaron jiragen saman Indiya sun datse wasu abubuwa a lokacin da wutar lantarkin ta tashi sakamakon fashe-fashen da aka yi a Jammu.

Lamarin dai ya kara tabarbarewa ne bayan da rundunar sojin Pakistan ta ce a daren jiya Indiya ta harba makamai masu linzami kan sansanonin sojinta guda uku, lura da cewa wasu makamai masu linzami sun fada cikin yankin Indiya.

"labari mai ban tsoro"

"Ina so in sanar da ku labarin mai ban mamaki cewa Indiya ta harba makamai masu linzami guda shida daga Udhampur, daya daga cikinsu ya sauka a Udhampur, sauran biyar kuma sun sauka a gundumar Amritsar da ke Punjab, Indiya" cewar kakakin sojin Pakistan a wata sanarwa ta ba-zata da aka watsa a gidan talabijin na kasar da yammacin ranar Juma'a.

A halin da ake ciki, Hakimin Amritsar a cikin wani sako da ya aikewa mazauna yankin a wayarsu ya ce, "Babu bukatar tsoro, Sirens suna ta hargitse, kuma muna cikin shirin ko ta kwana.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, wasu bama-bamai guda hudu sun afku a birnin Amritsar na kasar Indiya.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Pakistan ta fitar ta ce, "Indiya ta ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri ta hanyar harba makamai masu linzami kan muhimman wurare na sojojin Pakistan," tare da yin nuni da cewa, dakarun tsaron sama sun kame akasarin wadannan makamai masu linzami, kuma wadanda ba a kama su ba sun kasa kaiwa ga inda aka kai musu hari.

Ya kara da cewa, "Dole ne Indiya ta shirya yadda za mu mayar da martani, kuma sojojinmu a shirye suke su kare yankinta, sararin samaniyarta, da tsaron kasa".

A halin da ake ciki kuma kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton jin karar fashewar wasu abubuwa a birnin Peshawar dake arewa maso yammacin Pakistan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha